Yan bindiga sun kashe Shugaban makarantar Taraba sabon hari da suka kai Wukari

Yan bindiga sun kashe Shugaban makarantar Taraba sabon hari da suka kai Wukari

- Yan bindiga sun kashe shugaban makarantar sakandare na gwamnati na Tsokundi, mai suna Yusuf Yaro a wani sabon hari da suka kai hanyar Wukari-Tsokundi da ke karamar hukumar Wukari a jihar Taraba

- Marigayin na a hanyarsa na tafiya tare da sauran mutane lokacin da wasu yan bindiga suka kai masu harin bazata da misalin karfe 8:00 na safiyar ranar Talata

- Kakkakin yan sandan jihar, DSP David Misal, ya tabbatar da lamarin cewa maharan sun kashe mutum daya yayinda wani y ji rauni da harbin bindiga

Rahotanni sun kawo cewa an kashe shugaban makarantar sakandare na gwamnati na Tsokundi, mai suna Yusuf Yaro a wani sabon hari da aka kai hanyar Wukari-Tsokundi da ke karamar hukumar Wukari a jihar Taraba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa marigayin na a hanyarsa na tafiya tare da sauran mutane lokacin da wasu yan bindiga suka kai masu harin bazata da misalin karfe 8:00 na safiyar ranar Talata, 12 ga watan Nuwamba, inda suka kashe shugaban makarantar a nan take, yayinda abokan tafiyarsa suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Harin na zuwa ne yan makonni bayan yan kabilun Jukun da Tiv sun kulla yarjejeniyar ajiye makamansu.

Wani idon shaida a yankin, Mista Bulus Adi, ya bayyana cewa maharan sun zo ne daga cikin Jaji sannan suka bude wuta a kan matafiya inda daga bisani suka gudu suka koma jejin.

Mista Bulus ya zargi mayakan Tiv da kai harin, inda ya kara da cewa an dawo da zaman lafiya yankin yayinda aka zuba yan sanda da sojoji.

Shugaban karamar hukumar Wukari, Mista Adi Daniel ya fada ma majiyarmu cewa “yan bindiga sun kai hari hanyar Tsokundi-Wukari da misalin karfe 8:00 na yau sannan sun kashe wasu matafiya ciki harda Shugaban makarantar sakandare na Tsokundi.”

KU KARANTA KUMA: Kotun daukaka kara ta sake tsige wani dan majalisa na APC a Kwara

Da aka tuntube shi, kakkakin yan sandan jihar, DSP David Misal, ya tabbatar da lamarin cewa maharan sun kashe mutum daya yayinda wani y ji rauni da harbin bindiga.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel