Aminin Mamman Daura ya fallasa rade-radin karfin ikonsa a mulkin Buhari

Aminin Mamman Daura ya fallasa rade-radin karfin ikonsa a mulkin Buhari

Yayin da ake zargin cewa Malam Mamman Daura ne ke rike da madafan iko a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sam Nda-Isiah, ya fito ya yi karin-hasken da ba a sani ba.

‘Dan jaridar ya yi wani dogon rubutu domin taya Dattijon murnar cika shekaru 80 da haihuwa. Mista Sam Nda-Isiah, ya bayyana cewa Malam Daura bai tsoma bakinsa a cikin mulkin kasar.

Babban Marubuncin ya kuma kara da cewa shugaban kasa Buhari ne ya zabi Abba Kyari a matsayin shugaban ma’aikatan fadar sa a maimakon yadda wasu ke rayawa cewa aikin Daura ne.

A dogon rubutun da Marubucin ya yi, ya bayyana cewa Malam Mamman Daura da wasu Dattawan Arewa sun taba yunkurin tsaida wani Kiristan Arewa a matsayin mataimakin shugaban kasa.

A cewar Nda-Isiah, Daura da wasu masu fada-a ji a yankin Arewacin kasar sun nemi Janar T.Y Danjuma ya zama matamakin shugaba Goodluck Jonathan bayan rasuwar Ummaru ‘Yaradua.

KU KARANTA: Matasa sun huro wuta bayan sallamar Hadiman Osinbajo

A rubutun ‘dan jaridar, ya nuna cewa manyan na Arewa sun ji tsoron Danjuma ba zai karbi tayin da aka yi masa ba saboda ganin Goodluck Jonathan ba sa’ar sa bane da cewar rainin ya yi yawa.

Shugaban jaridar Leadership ya ce a lokacin da tsohon shugaban kasa Ummaru ‘Yaradua ya cika, an zabi Ahmed Makarfi, Babangida Aliyu, da Ibrahim Shema su maye gurbin Dr. G. Jonathan.

Yayin da Namadi Sambo ya ke kokarin ganin an zabi Ahmed Makarfi, sai kwatsam TY Danjuma ya ba da shawarar a dauki gwamnan na Kaduna a lokacin. A karshe kuma hakan aka yi a kasar.

Bayan haka, Nda-Isiah ya ce babu sa hannun Daura wajen zaben Ministocin shugaba Buhari. A cewarsa wani karamin Minista kadai ya ci albarkacin Daura a 2015, kuma yanzu an yi waje da shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel