Sojojin Sama Sun Samu Gagarumar Nasara kan Tsagerun 'Yan Boko Haram a Borno
- Rundunar sojojin saman Najeriya ta kai hare-hare kan tsagerun 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram a jihar Borno
- Jiragen yaki na rundunar sun yi ruwan wuta kan wata sananniyar maboyar 'yan ts'adda da ke a yankin Tumbuns na jihar Borno
- Rundunar ta bayyana cewa an kai hare-haren cikin kwarewa kuma sun samu gagarumar nasara wajen yin barna ga 'yan ta'addan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta kai hare-hare kan 'yan ta'addan Boko Haram a Borno.
Rundunar sojojin saman ta bayyana cewa ta yi nasarar lalata maboyar ’yan ta’adda a yankin Kudancin Tumbuns na jihar Borno.

Source: Getty Images
Tashar Channels tv ta kawo rahoton cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan hulda da jama'a da yada labarai na rundunar NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar a ranar Asabar, 25 ga watan Afirilun 2026.
Sojojin sama sun farmaki 'yan ta'adda
Sanarwar ta nuna cewa an samu wannan nasara ne ta hannun sashen rundunar sojojin sama na Operation Hadin Kai.
A cewar sanarwar, rundunar ta ci gaba da matsa lamba ta hanyar gudanar da wani samame na musamman na kai hari daga sama a ranar Juma’a, 24 ga Afrilu, 2026, da misalin karfe 6:50 na yamma a yankin Ali Sheriffti, wata sananniyar maboyar ’yan ta’adda a Kudancin Tumbuns.
“Bisa bayanan sirri masu tushe game da ayyukan ’yan ta’adda, jiragen yakin NAF sun gudanar da sintiri na musamman, inda aka hango wasu ’yan tada kayar baya suna zirga-zirga a wasu boyayyun hanyoyi."
"An bi sawunsu har zuwa wasu gine-gine da aka boye a karkashin duhun bishiyoyi, wanda hakan ya tabbatar da yunkurin boye kansu da gangan. Bayan an tantance su, NAF ta kai harin da ya dace, inda ta ragargaji gine-ginen da makamai.”

Kara karanta wannan
Za a gurfanar da sojoji 36 da ake zargi da yunkurin yi wa Tinubu juyin mulki gaban kotu
“Samamen ya cimma nasarar da ake bukata, inda aka lalata gine-ginen ’yan ta’adda, tare da kara tauye karfinsu da ’yancin zirga-zirga a yankin."
- Ehimen Ejodame

Source: Original
Sojoji za su ci gaba da ragargazar 'yan ta'adda
Rundunar ta lura cewa harin ya jaddada ci gaba da jajircewarta na yin amfani da bayanan sirri da hare-hare na musamman da nufin hana ’yan ta’adda wuraren buya, jaridar The Punch ta kawo rahoton.
Babban hafsan sojojin sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya sake tabbatar da wannan kuduri, inda ya bayyana cewa:
“Rundunar sojojin saman Najeriya za ta ci gaba da bin sawu da tarwatsa hanyoyin sadarwar ’yan ta’adda cikin kwarewa da karsashi, tare da tabbatar da cewa babu wata maboya da za ta kasance ba za mu iya kaiwa gare ta ba.”
Ya kara da cewa za a ci gaba da gudanar da ayyukan cikin tsanani don kare kasar nan da mutanenta.
Dakarun Sojojin sama sun hallaka 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun samu nasarar hallaka 'yan ta'addan ISWAP a Borno.
Dakarun sojojin sun kashe sama da ‘yan ta’addan ISWAP 30 a jerin wasu hare-hare da aka kai a yankin Tafkin Chad na jihar Borno.
Hare-haren da sojojin suka kai sun kuma yi sanadiyyar lalata jiragen ruwan da 'yan ta'addan suke yin amfani da su wajen yin zirga-zirga.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

