UK: Matashiya Deborah Longe ta na harin matsayin MP a Walthamstow
Yayin da wasu ‘Yan Najeriya ke jawowa kasarsu bakin jini, akwai wadanda su ke jawowa kasar abin alfahari a fadin Duniya. Daga ciki akwai Miss Deborah Longe mai shekaru 18 da haihuwa.
Deborah Longe wanda ‘Yar Najeriya ce da aka haifa a Turai, ta na neman takarar kujerar majalisa a Ingila. Matashiyar ‘Dalibar ta fito takarar Mazabarta watau Walthamstow a zaben da za ayi.
Longe wanda yanzu haka ta ke karatun Digiri a fannin shari’a a Jami’ar Durham ta yi alkawarin taimakawa ‘Yanuwanta Bakake idan har ta samu wannan kujera da ta ke nema a zaben bana.
Budurwar ta fito ta yi jawabi game da takararta a shafin Facebook, inda ta ce: “Jam'iyyar hadakar Kiristoci, CPA, sun zabe ni in tsaya takara a gundumar Walthamstow a babban zabe mai zuwa.”
CPA ce kadai jam’iyyar da ta dauki aure ibadar ubangiji domin kawo cigaba a gidaje. Jam’iyyar kuma ta na da manufar rage yawan zubar da ciki har a kai zuwa lokacin da za a daina gaba daya.
KU KARANTA: Za a shimfida shararra tun daga Najeriya har kasar Aljeriya - Fashola
Bugu da kari wannan jam’iyya ta CPA da ta ba ‘Yar ainihin Najeriyar tikiti ta na da muradin ganin an cusawa kananan yara ilmin jima’i a makaranta tare da goyon bayan ficewar kasar daga EU.
Ganin tsadar yakin neman zabe, yanzu wannan bakar fatar ta fara neman gudumuwar jama’a na akalla fam €500 domin ta iya tsayawa takara a zaben da za ayi a tsakiyar Watan Disamban gobe.
Miss Longe ta ce za ta yi amfani da gudumuwar da jama’a su ka bada ne wajen wallafa takardun kamfe domin yakin neman zabe a yankin Walthamstow da ke Arewa maso Gabashin Landan.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng