Allah mai iko: Makauniya ta rubuta Qur'ani daga Bakara har Nasi

Allah mai iko: Makauniya ta rubuta Qur'ani daga Bakara har Nasi

- Ikon Allah ba ya karewa. A kasar India ne aka samu mace makauniya da ta rubuta Qur'ani cikakke

- Makauniyar ta nuna bukatar koyon karatun Qur'an ne tun tana kwaleji amma babu malami mai koyar da ita

- Daga bisani ta samu malami mai suna Hafeez Mohammed wanda ya koyar da ita, cikin shekaru uku kuwa ta kammala rubuta Qur'ani

Wata mata 'yar asalin kasar India mai fama da cutar makanta ta rubuta Al-Qur'ani mai girma daga Bakara har Nasi da rubutun Braille.

Nafees Tasreen, malama ce a wata makarantar gwamnatin a India, ta kasance mai kwazo da sadaukarwa a harkokinta.

Kamar yadda Nafees Tasreen ta ce, a lokacin tana kwaleji, tana da son karanta Qur'ani amma bata samu malamin da ke son koyawa makauniya karatu ba.

Amma daga baya ta samu Hafiz Mohammed Tasleem kuma ya amince da zai dinga koya mata. A lokacin da take koyon karatun Qur'anin, ta nuna bukatar koyon rubuta Qur'ani da yaren Braille don taimakawa makafi irinta. Ta maida hankali wajen kokarin taimakon makafi irinta wajen karatu da fahimtar Qur'ani.

KU KARANTA: To fah: Wani saurayi ya koka akan yadda 'yan sanda suka yi kunnen uwar shegu da shi bayan 'yammata uku sun yi masa fyade

Nafees Tasreen ta dau shekaru uku ne wajen rubuta Qur'ani tare da fassarar sa a yaren Hindi. Bayan kammala rubuta Qur'ani, ta dau lokaci ana duba mata kura-kurenta.

Babban malamin kasar India ya jinjinawa aikinta kuma ya tabbatar da babu kura-kurai a duk surorin da ta rubuta.

Braille dai yanayin rubutu ne da Louis Braille ya kirkiro dashi wanda ke ba makafi damar rubutu da karatu.

Hakazalika, musulmai da yawa sun yarda cewa nakasa jarabawa ce daga Allah a rayuwa kuma zata iya zama baiwa a wani bangaren. Akwai bukatar duk mai nakasa ya kasance mai hakuri kuma a daina waresu don duba daga cikin wani bangare na al'umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel