Gwamnatin jihar Adamawa ta kori ma'aikata fiye da 300

Gwamnatin jihar Adamawa ta kori ma'aikata fiye da 300

A ranar Talata ne aka damka wa ma'aikatan kwalejin kimiyya ta jihar Adamawa takardar sallama daga aiki.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa ma'aikatan da aka kora sun hada da masu koyar wa da sauran ma'aikata da aka dauka a tsakanin 2017 zuwa 2019.

Mukaddashin rijistaran makarantar, Uwargida Rebecca Kinjir, wacce ta saka hannu a kan takardun korar ma'aikatan, ta ce sallamar ma'aikatan biyayya ce ga umarnin kwamitin da gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya nada a kan makarantar.

Wasikar sallamar ta umarci ma'aikatan da abin ya shafa da su mika duk wani kayan makarantar da ke hannunsu ga hukumar makarantar kafin su tafi.

"Kwamitin da mai girma gwamna, Alhaji Ahmadu Fintiri, ya kafa ya amince da a janye aikin da aka baka bayan ziyarar da ya kawo.

"Ana bukatar ka mika duk wasu kayayyakin makaranta da ke hannunka ga shugaban bangaren da kake aiki bayan ka samu wannan wasika

DUBA WANNAN: Sunayen kwamishinonin 'yan sanda 13 da suka samu karin girma zuwa AIG

"Hukumar wannan makaranta na mika godiya gare ka a kan gudunmawar da ka bayar a tsawon wa'adin da ka shafe kana aiki," kamar yake a cikin wasikar.

Gwamnatin sabon gwamnan jihar Adamawa, Ahmed Fintiri, ta zargi tsohuwar gwamnatin jihar a karkashin tsohon gwamna, Muhammadu Bindow, da daukan ma'aikata ba bisa ka'ida ba kuma a kurarren lokaci.

Saboda hakan ne gwamnatin ta kafa kwamiti domin ya ziyarci dukkan manyan makarantun jihar domin bayar da shawara a matakin da ya kamata a dauka a kan sabbin ma'aikatan da aka dauka a makarantun.

(NAN)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel