Latest
Buhari ya bayyana cewa bude iyakokin kasar ya dogara ne a kan rahoton kwamitin bangare uku da ya hada da gwamnatocin Najeriya, na jamhuriyar Benin dana jamhuriyar Nijar.
Ministar harkokin agaji da hana annoba da kuma ci gaban al’umma, Sadiya Umar Farouq ta yi bayanin dalilin da yasa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi afuwa ga mayakan Boko Haram da suka shiryu.
Ramalan Yero ya na ganin cewa ‘Yan siyasa su na da hannu a kan matsalar rashin tsaro. Wanda ya ce abubuwa biyu su ka kawo rashin tsaro a kasar nan.
Wani Mutum ya kuma kamuwa da cutar zazzabin Lassa a Kaduna a Arewacin Najeriya. Yanzu haka Jihar Kaduna ta na wayar da kan jama’a game da cutar.
Gwamnatin Buhari ta bayyana Yankin Arewa da cewa ya fi ko ina fama da talauci a Najeriya. Mai martaba Sarkin Birnin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya saba wanna magana.
PDP ta ce kokarin ba Gwamnan Kebbi $100m daga dukiyar satar Abacha ya tonawa Buhari asiri don haka aka nemi ayi gwamnatin Buhari cikakken bincike.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya baiwa kamfanin da shi ne diraktanta kwangilan kudi sama da bilyan uku da rabi , kuma hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa ga masu rike da mukaman mulki, Premium Times ta ruwaito.
Yan ta'addan Boko Haram sun kona barikin yan sanda, cocina, gidan Janar Paul Tarfa da gidajen mutane a mumunan harin da suka kai jihar Adamawa ranar Juma'a, 21 ga watan Febrairu, 2020.
Sanata Ahmed Sani Yariman-Bakura ya ce Gwamnan Zamfara zai koma APC. Yanzu haka dai tsohon Sanatan APC ya koma Makarantar addini bayan ya bar Majalisa.
Masu zafi
Samu kari