"Ban Cire Rai ba": Sanusi II Ya ba ECOWAS Shawara kan Kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso

"Ban Cire Rai ba": Sanusi II Ya ba ECOWAS Shawara kan Kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso

  • Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya sake dauko batun ficewar kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso daga kungiyar ECOWAS
  • Sanusi II ya bayyana cewa hadewar kasashen Afrika ta Yamma a inuwa guda yana da matukar muhimmanci ga yankin
  • Mai martaba sarkin ya bukaci kungiyar ECOWAS da ta bi hanyar sasanci domin dinke barakar da ke tsakaninta da kasashen uku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ba kungiyar ECOWAS shawara kan kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso.

Sanusi II ya buƙaci kungiyar ECOWAS) da ta bi sawun sasanci da ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso wadanda suka fice daga cikinta.

Sanusi II ya bukaci ECOWAS ta yi sasanci
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II a fadarsa Hoto: @masarautarkano
Source: Twitter

Sanusi II ya yi wannan kiran ne a wani taron lacca wanda cibiyar nazarin shari'a da dimokuradiyya ta kasa (NILDS) ta shirya ranar Alhamis, 25 ga watan Yunin 2026 a Abuja, rahoton Premium Times ya nuna hakan.

Kara karanta wannan

'Kashi 80 na matsalolin tsaro da suka addabi Sakkwato na da alaka da miyagun kwayoyi'

Me Sanusi iI ya ce ECOWAS ta rage karfi

Mai martaba sarkin ya ce ficewar ƙasashen Sahel guda uku ya raunana haɗin kan yankin, haɗin gwiwar tsaro, da kuma damammakin tattalin arziƙi a faɗin Afirka ta Yamma.

Ya bayyana Nijar a matsayin wani muhimmin gurbi na kariya tsakanin Najeriya da barazanar 'yan ta'adda da ke aiki a faɗin Libya, Algeria, da sauran sassan Afirka ta Arewa, jaridar Leadership ta kawo labarin.

Amfanin Nijar ga Najeriya

Ya lura cewa tsarin tsaron ƙasa na Najeriya a tarihi ya dogara ne ga haɗin gwiwa da Nijar, wanda hakan ya sa rashin hulda da ƙasar ya zama babban abin damuwa na fannin tsaro.

Tsohon gwamnan babban bankin na Najeriya (CBN) ya tuna da tallafin da Nijar ta ba Najeriya lokacin yaƙin basasa, inda ya lura cewa shugabannin baya sun ba da fifiko ga haɗin kan yankin duk da matsin lamba da rarrabuwar kai na ƙasa da ƙasa.

Ya ce an yi ƙoƙari na diflomasiyya domin hana gurɓacewar dangantaka, inda ya ƙara da cewa kuskuren da wasu manyan jarumai suka yi ya taimaka wajen haifar da rikicin.

Kara karanta wannan

Bayan Boko Haram, ISWAP da Lakurawa, sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta bayyana a Arewa

Ya bukaci a sasanta

Sanusi II ya buƙaci gwamnatoci, shugabannin addini, ƙungiyoyin fafutukar jama'a, da 'yan ƙasa da su ci gaba da tuntuɓar takwarorinsu na ƙasashen da abun ya shafa domin tabbatar da sasanci.

“Haɗin kan ƙasashe 15 ya fi na ƙasashe 12 kyau. Dunkulalliyar Afirka baki ɗaya ya fi kawai a ce Afirka ta Yamma."

- Muhammadu Sanusi II

Sarkin ya bayyana cewa ECOWAS tana iya aiki ba tare da ƙasashe guda uku ba, amma za ta rasa gagarumar fa'ida da ke tattare da faɗaɗa haɗin gwiwar yanki da kasuwanni.

A cewarsa, Najeriya tana da amfanin da za ta samu mai yawa ta hanyar sauya ƙasashen maƙwabta su zama ingantattun kasuwannin fitar da kayayyaki ta hanyar tabbatacciyar dangantakar siyasa.

Sanusi II ya ba kungiyar ECOWAS shawara
Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a fadarsa Hoto: @masarautarkano
Source: Twitter

Sanusi II fatan ganin an koma wuri guda

Sanusi II ya ce Shugaba Bola Tinubu ya fuskanci mawuyacin yanayi lokacin rikicin Nijar, kasancewar ya karbi mulki ba tare da nada ministoci ba.

Kara karanta wannan

"Ba mu ji dadi ba"; Wike ya aika sako ga Super Eagles kan gaza zuwa gasar cin kofin duniya

Ya lura cewa haƙuri da tattaunawa za su iya samar da mafita mafi hanzari, inda ya jaddada cewa har yanzu akwai kyakkyawar niyya mai yawa tsakanin shugabannin yankin.

“Har yanzu ina tsammanin akwai babbar yuwuwar samun sasuwanci. Ban yanke ƙauna ba baki ɗaya.

- Muhammadu Sanusi II

Sanusi II ya roki EU kan Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai martaba sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya mika bukatarsa ga kungiyar tarayyar Turai (EU).

Muhammadu Sanusi II ya buƙaci kungiyar tarayyar Turai ta faɗaɗa tallafin da take bai wa jihar Kano da Najeriya baki daya.

Basaraken ya jero muhimman fannoni da ke bukatar tallafin wadanda suka haɗa da tsaro, kiwon lafiya da ilimi da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng