AGF: Abubuwan more rayuwa za a gina da kudin satar Abacha da aka dawo da su

AGF: Abubuwan more rayuwa za a gina da kudin satar Abacha da aka dawo da su

Ministan shari’a kuma babban Lauyan gwamnatin Najeriya, Abubakar Malami SAN, ya ce aiki za a yi wa ‘Yan kasa da kudin satar Sani Abacha da aka dawo da shi.

Abubakar Malami ya yi wannan jawabi ne ta bakin Hadimin da ke taimaka masa wajen hulda da jama’a, Dr. Umar Gwandu, inda ya musanya rahotannin da ke yawo.

Ministan ya bayyanawa Manema labarai cewa sam babu wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnan jihar Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu ko ma wani.

Malami ya nuna rade-radin da aka ji na cewa Najeriya za ta ba wani Mutum dala miliyan 100 daga cikin kudin satar Sani Abacha da aka karbo daga hannun kasar Amurka.

A cewar Ministan, Atiku Bagudu ya na kara a kasar Amurka inda ya ke neman hakkinsa a cikin kudin da ake zargin Marigayi Sani Abacha da sacewa daga asusun Najeriya.

KU KARANTA: Ya kamata a binciki Buhari game da kudin satar Abacha - PDP

AGF: Abubuwan more rayuwa za a gina da kudin satar Abacha da aka dawo da su
Gwamna Bagudu bai da kaso cikin kudin da Najeriya za ta karba - Malami
Asali: Facebook

Ana zargin Bagudu, wanda ya na cikin manyan jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, da hannu a badakalar Abacha, wanda hakan ya kai shi ga zama a gidan yari a Amurka.

Malami SAN ya ce gwamnatin Buhari ta na kokarin karbo dukiyar da James Ibori da Deziani Alison-Madueke su ka sace daga asusun kasa a lokacin da su ke mulki.

Har ila yau, Ministan kasar ya bayyana cewa za ayi amfani da wannan kudi wajen aikin hanyar Abuja zuwa Kano, da gadar Neja da kuma titin Legas zuwa Garin Ibadan.

“Babu wani mutum da aka yi da shi cewa za a ba shi kaso daga cikin wannan kudi a takardun da aka tattauna a kansu a majalisar zartarwar tarayya.” Inji Hadimin Ministan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel