An tabbatar da samuwar cutar Lassa a Jihar Kaduna - Kwamishina

An tabbatar da samuwar cutar Lassa a Jihar Kaduna - Kwamishina

A yayin da mutane su ke murnar cewa cutar Lassa ta lafa, labari ya zo mana cewa an sake samun labarin barkewar cutar kwanan nan a cikin jihar Kaduna.

Kwamishinar lafiya ta gwamnatin jihar Kaduna, Dr. Amina Mohammed-Baloni, ta tabbatar da cewa an samu wani Mutumi da ya kamu da wannan cuta.

Dr. Amina Mohammed-Baloni ta bayyana cewa wani Bawan Allah mai shekara 40 a Duniya ne ya kamu da wannan zazzabi, kuma yanzu haka ana kula da shi.

Amina Mohammed-Baloni ta ce a Ranar Juma’a, 21 ga Watan Fubrairun 2020, aka tabbatar da wannan labari a asibitin koyon aikin likita da ke Garin Shika.

Wannan maras lafiya da aka samu ya na nufin a halin yanzu akwai mutane biyu da su ke dauke da cutar a jihar Kaduna, bayan zazzabin ya sake dawowa gari.

KU KARANTA: An fara kiran a karbe kujerar Sanatan da ke cikin gidan yari

An tabbatar da samuwar cutar Lassa a Jihar Kaduna - Kwamishina
Jihar Kaduna ta na wayar da kan jama’a game da cutar Lassa
Asali: Twitter

A cewar Kwamishinar harkar kiwon lafiyar, a jihar Kaduna, an samu mutane takwas daga cikin 74 da ake zargin sun kamu da wannan cuta a fadin Najeriya.

Daga cikin wadanda su ka kamu da zazzabin a jihar Kaduna, an rasa Maras lafiya daya, wanda ya rasu a sakamakon rashin daukar matakin da ya dace tun wuri.

An maida marasa lafiya biyu gidajensu bayan sun samu sauki, sun kuma rabu da cutar. Sauran biyun kuma an gano su na dauke da cutar ne bayansu mutu.

“Haka zalika na shida daga cikin marasa lafiyan ya zo ne daga tafiya daga Ebonyi, kuma yanzu haka ya na killace a dakin kula da wannan cuta da ke jihar.”

Kwamishinar ta bayyana cewa wani daga cikin Marasa lafiyan da ya dauko cutar a jihar Kebbi, ya mutu a gadon asibitin koyon aiki na Ahmadu Bello da ke Shika.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel