NAF ta kashe manyan shugabannin ISWAP a Borno

NAF ta kashe manyan shugabannin ISWAP a Borno

Rundunar Sojojin Saman Najeriya (NAF) a jiya ta ce ta kashe wasu muhimman shugabannin kungiyar slamic State of West Africa Province (ISWAP) a Jubillaram da Alinwa a arewacin Borno.

Wannan na zuwa ne bayan da dakarun sojojin Operation Hadarin Daji a Zamfara suka kashe 'yan bindiga 13 kuma suka kama wasu takwas a jihar Zamfara.

Direktan watsa labarai na NAF, Ibikunle Daramola a jiya a Abuja ya ce dakarun mayakan sama (ATF) na Operation Lafiya Dole karkashin atisayen Operation Rattle Snake III sun kai wa shugabanin ISWAP hari a lokacin da suka hadu wurin taro bayan samun bayannan sirri.

DUBA WANNAN: Atiku ya yi magana a kan harin da Boko Haram ta kai Adamawa

Sai dai sanarwar ba ta fadi adadin wadanda aka kashe ba da mukamansu a kungiyar amma ta kara da cewa: "An kai harin ne bayan samun bayyanan sirri da ke nuna wasu muhimman shugabanin ISWAP sun hadu domin yin taro a wurare biyu a Jubillaram da Alinwa a karamar hukumar Marte.

"Kazalika, dakarun na ATF sun kai hare-hare a wurare daban-daban inda suka yi raga-raga da wuraren taron 'yan ta'addan," inji Daramola. Ya ce an kai hare-haren ne a sumamen da aka kai a ranar Alhamis.

Daramola ya ce NAF tare da hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro za ta cigaba da yi wa 'yan ta'addan lugwuden wuta a yankin na Arewa maso Gabas domin tallafawa sojojin da ke aikin ragargazan 'yan ta'addan a kasa.

A cewarsa, ya ce Operation Rattle Snake da aka fara a ranar 4 ga watan Fabrairu an kafa shi ne domin tarwatsa sansanin 'yan ta'addan da ke arewa maso gabas domin taimakawa yaki da 'yan ta'addan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel