Kwamiti a majalisar wakilai ya yi wa wasu ministoci 4 kiran gaggawa

Kwamiti a majalisar wakilai ya yi wa wasu ministoci 4 kiran gaggawa

- Majalisar wakilai ta yi wa wasu ministocin kasar nan hudu kiran gaggawa zuwa gaban wani kwamitinta

- Majalisar na zargin ma'aikatun ne da rashin kare bayanin kashe kudinsu na wani tsawon lokaci

-Ministocin sun hada da na kiwon lafiya, noma da kiwo, karamar ministar sufuri da kuma na kasuwanci da zuba hannayen jari

Majalisar wakilai ta yi wa wasu ministoci hudu kiran gaggawa zuwa gaban wani kwamitinta don amsa tambayoyi a kan wasu cibiyoyin da ke kasan su. Cibiyoyin da ke kasansu sun gagara kawo rahotanni kan bayanin kudin da suka shiga asusunsu ta ofishin babban akawun kasar nan.

Kwamitin na bukatar cibiyoyin da su gurfana gabanta tare da kungiyoyin gudanarwarsu, kasafin kudinsu na shekara da kuma bayanin kashe kudinsu wanda ya shafe na tsawon lokacin da ake bincike.

Majalisar na bincikar abinda ta kwatanta da ganganci wajen kin bada bayanin kudin da suka kashe daga 2014 zuwa 2018, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kwamiti a majalisar wakilai ya yi wa wasu ministoci 4 kiran gaggawa
Kwamiti a majalisar wakilai ya yi wa wasu ministoci 4 kiran gaggawa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Muhimman abubuwa game da Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum

Ministocin sun hada da ministan lafiya, Dr. Osagie Ehanire, Ministan aikin gona, Alhaji Sabo Nanono, ministan kasuwanci da hannayenn jari, Otunba Niyi Adebayo da kuma karamar minister sufuri, Sanata Gbemisola Saraki.

Saraki za ta bayyana gaban kwamitin ne da babban sakataren ma’aikatar a kan kin bayyanar daraktan NIMASA gaban kwamitin don bayanin kudin da suka kashe tun 2014.

Shi kuwa ministan aikin gona zai bayyana gaban kwamitin ne tare da duk cibiyoyin da ke kasan ma’aikatar don bayanin tsaikon da aka samu na hada kwamitin gudanarwa na cibiyoyin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng