Rashin Tsaro: Gwamna Ya Bukaci a Haramta Almajiranci a Najeriya
- Rahoto ya nuna cewa Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bukaci majalisar dokoki ta kasa ta haramta tura yara almajiranci baki daya a Najeriya
- Gwaman ya ce tsarin almajiranci na cikin manyan abubuwan da ke kara yawan yaran da ba su zuwa makaranta a Arewa tare da ta'azzara rashin tsaro
- Abdullahi Sule ya ba da shawarar maye gurbin tsarin wajabta ilimin boko da kuma koyar da sana'o'in hannu domin bai wa yara hanyar dogaro da kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bukaci majalisar dokoki ta kasa da ta haramta tsarin Almajiranci baki daya.
Ya yi magana yana mai cewa tsarin na ci gaba da zama babban abin da ke haddasa karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta a Arewacin Najeriya da kuma ta'azzarar matsalolin tsaro.

Kara karanta wannan
Kano ta yi zarra, ta fi dukkan jihohin Najeriya sababbin masu rijistar katin zaɓe

Source: Facebook
Leadership ta wallafa cewa Gwamna Sule ya yi wannan kira ne a Abuja yayin taron inganta rayuwar dan Adam a Arewacin Najeriya.
Kiran haramta almajiranci a Najeriya
Gwamna Abdullahi Sule ya nemi 'yan majalisa da shugabannin Arewa su dauki matakan kafa dokoki da za su kawo karshen tsarin almajiranci tare da maye gurbinsa da ilimin boko da shirye-shiryen koyar da sana'o'i.
A cewarsa, Najeriya na fuskantar matsananciyar matsalar ilimi, inda aka kiyasta cewa yara miliyan 18.3 ne a halin yanzu ba sa zuwa makaranta, yayin da tsarin Almajirai ke kasancewa "babban ginshikin da ya fi kowanne haddasa matsalar."
Da yake yin nuni da alkaluman baya-bayan nan, Sule ya ce Almajirai sun kai tsakanin kashi 72 zuwa 81 cikin 100 na jimillar yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, inda mafi yawansu ke zaune a jihohin Arewa.

Source: Facebook
Alakar almajiranci da tsaro
Gwamnan ya yi gargadin cewa illolin tsarin ba su tsaya kan bangaren ilimi kadai ba, domin yana da alaka kai tsaye da matsalolin tsaron yankin.

Kara karanta wannan
Majalisar Dattawa ta amince da bukatar Tinubu kan batun kafa yan sandan jihohi a Najeriya
Ya ce yawancin kananan yara da ake jan hankalinsu zuwa ayyukan 'yan bindiga da sauran laifuffuka sun fito ne daga tsarin Almajiranci, yana mai jaddada cewa akwai bukatar daukar matakin gaggawa.
Sule ya bayyana cewa jihar Nasarawa tana da kimanin yara 430,000 da ba sa zuwa makaranta, yana mai cewa gwamnati kadai ba za ta iya magance matsalar ba, sai da hadin gwiwar masana, shugabannin siyasa da cibiyoyin gargajiya.
Ya tunatar da yadda jihohin Nasarawa da Kaduna suka mayar da dubban Almajirai zuwa jihohinsu a shekarar 2020, yana mai cewa duk da cewa matakin ya zama dole a lokacin, bai samar da mafita mai dorewa ga matsalar ba.
AIT ta wallafa a X cewa ya ce matakan tilastawa dole ne su kasance tare da samar da hanyoyin da za su tabbatar da samun ilimi da damar rayuwa ga matasa.
Ya kuma bukaci shugabannin Arewa da masu ruwa da tsaki su mayar da shawarwarin da aka tattauna a taron zuwa kudurorin dokoki domin gabatar da su ga majalisar dokoki ta kasa.
Gwamna Sule ya yi huduba
A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya jagoranci hudubar sallar Juma'a a wani sabon masallaci.
Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Ahmadu Adamu Muazu ne ya gina masallacin domin ya zamo sadaka mai gudana ga mahaifiyarsa da ta rasu.
Manyan mutane ciki har da ministan ilimi, Dr Tunji Alausa na cikin wadanda suka hallara masallacin da Adamu Muazu ya gina a Nasarawa.
Asali: Legit.ng
