An harbe ‘Dan wasan kungiyar Reno, Tiyamiyu Kazeem a Sagamu

An harbe ‘Dan wasan kungiyar Reno, Tiyamiyu Kazeem a Sagamu

Ana ta samun mabanbantan labari a game da ‘Dan wasan kwallon kafan kungiyar Reno da aka harbe a kudancin Najeriya a cikin karshen wannan makon.

An tabbatar da cewa an harbi Tiamiyu Kazeem da bindiga a jiya. Kazeem ya kasance ya na bugawa kungiyar Remo Stars da ke jihar Ogun wasa kafin a kashe shi.

Kungiyar Remo Stars ta bayyana cewa za ta yi bakin kokarinta wajen ganin an gudanar da bincike game da mutuwar tsohon Tauraron na ta, Tiamiyu Kazeem.

Kulob din ya yi wannan bayani ne a wani gajeren jawabi da ya fitar a shafin Tuwita, inda ya tabbatar da mutuwar ‘Dan wasan, sannan ya mika ta’aziyyarsa.

Mun samu labari daga gidan talabijin na Channels TV cewa Kwamishinan ‘Yan Sanda ya bada umarnin kama Jami’in da ya yi sanadiyyar mutuwar ‘Dan wasan.

KU KARANTA: 'Yan Shi'a sun tada rikici, sun harbi 'Yan Sanda a Majalisa

An harbe ‘Dan wasan kungiyar Reno, Tiyamiyu Kazeem a Sagamu
Ana zargin SARS da harbe ‘Dan kwallon Reno Stars
Asali: Twitter

Kawo yanzu ba a san wani ‘Dan Sanda ne ya harbi ‘Dan wasan kwallon kafan ba. A dalilin kashe shi, an yi zanga-zanga a ofishin ‘Yan Sanda da ke Garin Sagamu.

Rahotanni sun ce a Ranar Asabar da rana tsaka wani Jami’in SARS ya tare Marigayin yayin da ya ke tuki a mota tare da wani ‘Dan wasan kungiyarsa, Sanni Abubakar.

Wannan jami’in tsaro ya zargi Kazeem da cewa ‘Dan damfara ne shi. A dalilin haka, ‘Dan wasan kwallon ya fito da katin kungiyar kwallo domin ya gabatar da kansa.

Duk da haka wannan Jami’i na SARS bai gamsu da bayanin ‘Dan wasan ba, sai ya fito da shi daga cikin motarsa. A na haka ne sai kwastam harsashin bindiga ya same shi,

Kakakin ‘Yan Sandan Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya karyata wannan labari, ya ce ba haka abin ya faru ba, ya ce bindigar ‘Yan Sanda ta samu matsala ne har ta saki harsashi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel