Zo Ku Nema: Kasar Ireland Ta ba 'Yan Najeriya Damar Yin Karatu Kyauta
- Gwamnatin Ireland ta sanar da bude shirin karatun digiri na biyu wanda zai ba ‘yan Najeriya damar yin karu kyauta a jami'o'in kasarta
- Shirin zai bai wa kwararru damar yin karatun digiri na biyu na shekara guda a manyan jami’o’in Ireland tare da cikakken tallafin kudi
- Dole ne wadanda za su nemi tallafin su kasance suna da digirin farko da akalla 'Second Class Lower', da shekaru uku na kwarewar aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Ofishin Jakadancin Ireland a Najeriya ya sanar da fara karbar takardun neman shiga shirin Ireland Fellows Programme 2026.
A karkashin wannan shirin, ‘yan Najeriya za su samu damar yin karatun digiri na biyu kyauta a kasar Ireland.

Source: Getty Images
Ireland ta bude tallafin karatu ga 'yan Najeriya
Ofishin jakancin Ireland ya yi wa 'yan Najeriya wannan babban albishir din ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a.

Kara karanta wannan
"Ba mu ji dadi ba"; Wike ya aika sako ga Super Eagles kan gaza zuwa gasar cin kofin duniya
Gwamnatin Ireland ta ce an tsara shirin ne domin wadanda suke da kwarewa da kuma wadanda ke tsakiyar matakin aiki daga Najeriya da Ghana.
A cewar sanarwar, shirin Ireland Fellows Programme na bai wa wadanda suka cancanta damar yin karatun digiri na biyu na tsawon shekara guda a manyan jami’o’in kasar.
Ofishin Jakadancin ya ce:
“An bude shirin Ireland Fellows Programme a ranar 29 ga Yuni 2026. Yi amfani da wannan damar domin yin karatun digiri na biyu a Ireland karkashin cikakken tallafin karatu.”
Sharuddan samun tallafin karatu a Ireland
Tallafin karatun ya kunshi kudin makaranta, kudin jirgi da biza, kudin alawus na wata-wata, tallafin masauki da kuma inshorar lafiya.
Wannan na nufin wadanda aka zaba za su samu cikakken tallafin gudanar da karatun ba tare da biyan manyan kudade daga aljihunsu ba.
Bayanan da jakadancin ya fitar sun nuna cewa wadanda za su nemi wannan damar dole su kasance ‘yan Najeriya ko Ghana masu zama a kasashensu.
Haka kuma dole su kasance suna da:
- Digiri na farko mai darajar da ta kai 'Second Class Lower'.
- Shekaru uku ko fiye na kwarewar aiki mai alaka da fannin da suke nema.
Dama ta musamman ga ‘yan Najeriya
Ga masu nema daga Najeriya, shirin ya hada da Roger Casement Fellowship da bangaren shirin 'Hakkin 'dan Adam', wanda ya fi mayar da hankali kan shirye-shiryen digiri na biyu a fannonin doka, kare hakkin dan Adam da shugabanci.

Source: Twitter
Ofishin jakadancin ya ce masu sha’awar shiga shirin za su iya samun cikakkun bayanai da yadda ake nema ta shafin intanet na Ireland Fellows Programme.
An bayyana cewa za a fara karbar takardun neman shiga shirin daga ranar 29 ga Yuni 2026, sannan za a rufe shafin neman tallafin ranar 26 ga Yuli 2026.
Masu sha’awar neman wannan damar za su mika bukatunsu ta shafin shirin Ireland Fellows Programme: https://irelandfellows.africa/.
Karanta sanarwar a nan kasa:
Amurka ta bude damar karatu kyauta
A wani labari, mun ruwaito cewa, Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya sanar da fara kwasa-kwasan koyon Turanci kyauta domin ƙara ƙwarewar sana’a.
Haka zalika an bayyana cewa shirin zai ba mutane daga kasashe fadada damar samun ayyukan yi a fannoni daban-daban a duniya.
An tsara kwasa-kwasan ne ta shirin OPEN na ma’aikatar harkokin wajen Amurka, inda mahalarta za su koyi darussa tare da hulɗa da masu koyo daga ƙasashe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

