Fitaccen Jarumin Fim a Najeriya, Momodu Ya Shiga Rundunar Sojin Kasar Amurka
- Fitaccen jarumin masana'antar fina-finan Nollywood ta Najeriya, Joseph Momodu ya sanar da shiga rundunar sojin Amurka
- Jarumin ya bayyana cewa tuni ya kammala daukar horon makonni 10 a Fort Leonard Wood don zama sojan kasar Amurka
- Ya ce nasarar ta kasance cikar burin da ya gada daga marigayi mahaifinsa, yana mai cewa ya fito da mukamin Specialist (SPC) a rundunar sojin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United States - Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Joseph Momodu, ya sanar da cewa ya shiga rundunar sojin Amurka.
Jarumin ya bayyana hakan a matsayin wata babbar nasara da kuma cikar burin da ya gada daga marigayi mahaifinsa.

Source: Facebook
Momodu ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Juma'a, 26 ga watan Yuni, 2026.
Ya ce ya kammala horon makonni 10 na Basic Combat Training a Fort Leonard Wood da ke jihar Missouri kafin aka dauke shi aiki a hukumance da mukamin jami'i na musamman (SPC) a rundunar.
Dalilin nasarar jarumi Momodu
Momodu ya ce wannan matsayi ya samu ne bayan dogon kokari, sadaukarwa da jajircewa da ya yi a tsawon lokacin daukar horo.
Ya rubuta cewa:
“Tun farko na yi imani da nasarar da ake samu ta hanyar cancanta. Wannan ne ya sa kullum nake kokarin dagewa na yi har abin da ya zarce iyakata."
A cewarsa, horon ya kasance mai matukar wahala, inda ya fuskanci gajiya, tsoro, damuwa, karancin barci, ruwan sama da zafin rana.
Yadda jarumin ya zama sojan Amurka
Jarumin ya amince cewa a wasu lokuta ya fara kokwanto game da kansa, amma bai taba daina hangen cikar burinsa ba.
Ya ce:
“Akwai lokutan da na tambayi kaina, waye ya sa na shiga wannan abu?’ Amma ban taba mantawa da inda nake son isa ba.”
“Mun yi horo ba kakkautawa, an karya mu sannan aka sake gina mu. Na kwanta a matsayin farar hula, na tashi a matsayin soja.”
A cewarsa, horon ya koya masa yadda mutum zai iya jure wahala domin samun nasara.
Momodu ya tuna da marigayi mahaifinsa
Momodu ya bayyana cewa shiga rundunar sojin Amurka na da muhimmanci a gare shi saboda ya ci gaba da abin da marigayi mahaifinsa ya fara.
“A ranar 12 ga Afrilu, 2026, na karrama marigayi mahaifina ta wata hanya ta musamman. Bayan shekaru 20 da rasuwarsa, na dauki tutar da ya bari a rundunar ‘yan sandan Najeriya, sannan na ci gaba da ita ta hanyar shiga rundunar sojin Amurka," in ji shi.

Source: Instagram
Momodu ya sadaukar da wannan nasara ga Ubangiji, marigayi mahaifinsa da kuma gidan sarautar Oba Momodu II na Avyuele Clan da ke Agbede, karamar hukumar Etsako West a jihar Edo.
Haka kuma ya mika godiyarsa ga ofishin daukar ma'aikatan rundunar sojin Amurka da ke Burbank a jihar California saboda taimakon da suka ba shi wajen shiga aikin.
Jarumar Nollywood ta shiga wani hali
A wani rahoton, kun ji cewa fitacciyar jarumar Nollywood, Doris Ogala, ta bayyana damuwa cewa watakila ba za ta daɗe a raye ba sakamakon halin da ta tsinci kanta a ciki.
Jarumar fim din ta fashe da kuka a wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, inda ta ce komai ba ya tafiya daidai a rayuwarta.
Doris Ogala ta bayyana mawuyacin halin da Fasto Chris Okafor ya jefa ta a ciki bayan tsawon lokaci suna soyayya da alkawarin aure.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


