Kashe biliyan N5 a kan sayen motoci: SERAP ta shigar da karar Gbajabiamila da 'yan majalisa

Kashe biliyan N5 a kan sayen motoci: SERAP ta shigar da karar Gbajabiamila da 'yan majalisa

SERAP tare da wasu masu kishin kasa 192 sun mika korafinsu gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja don hana kakakin majalisar dattijai, Femi Gbajabiamila da sauran 'yan majalisar dattijan a kan kashe naira biliyan 5.04 don siyan motocin alfarma.

SERAP na bukatar kotun da ta umarci hukumar majalisar dattijan kasar nan da kada ta saki kudin don siyan motocin alfarmar ga 'yan majalisar.

A karar da aka shigar a ranar Juma'a, SERAP da wasu 'yan Najeriya masu kishin kasa sun ce 'yan Najeriya na da hakki a kan dukiyar kasa da kuma yadda 'yan majalisar zasu dinga amfani da ita.

Sun kara da cewa babu hujjar da ta ce 'yan majalisar su zabi motocin alfarma daga ketare sannan su matsawa 'yan Najeriya siyan kayan cikin gida.

Kashe biliyan N5 a kan sayen motoci: SERAP ta shigar da karar Gbajabiamila da 'yan majalisa
Kashe biliyan N5 a kan sayen motoci: SERAP ta shigar da karar Gbajabiamila da 'yan majalisa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Muhimman abubuwa game da Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum

Masu karar sun kara da cewa, ba daidai bane 'yan majalisar su ki amince wa da wasu irin motocin masu arha yayin da 'yan Najeriya ke cikin tsananin talauci kuma gwamnatoci da yawa sun kasa biyan ma'aikata albashi ko kudin fansho.

Idan zamu tuna 'yan majalisar wakilan sun bayyana kudirinsu na siyan motocin alfarma 400 wadanda kowacce daga ciki ta kai $35,000 wanda jimillar su ta kai biliyan 5.04.

Wannan lamarin kuwa ya jawo cece-kuce daga 'yan Najeriya masu yawa. wasu na kallon matsalar tsaron kasar a abinda ya kamata a mayar da hankali tare da zubawa kudade ba wai siyan motocin alfarma ba da kudin baitul malin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel