Abacha: Kokarin dawowa Gwamnan Kebbi da $100m ya tonawa Buhari asiri – PDP

Abacha: Kokarin dawowa Gwamnan Kebbi da $100m ya tonawa Buhari asiri – PDP

Babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta yi kira ga Majalisar tarayya ta binciki gwamnatin tarayyar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke jagoranta domin ta ceci kasar nan.

Jam’iyyar PDP ta bukaci ayi wa gwamnatin APC binciken kurilla ne a game da rahotannin da ake ji na cewa ana kokarin daukar wasu daga cikin kudin da kasar Amurka ta dawo da su.

A Ranar Asabar, 22 ga Watan Fubrairun 2020, Sakataren yada labarai na jam’iyyar adawar, Kola Ologbondiyan, ya fito ya yi bayani, ya na zargin gwamnatin tarayya da rashin gaskiya.

Kola Ologbondiyan ya ke cewa bayanan da su ke fitowa a kan wannan gwamnati game da zargin aikata rashin gaskiya ya fallasa irin barna da satar dukiyar kasa da ake yi a mulkin APC.

PDP ta dogara ne da bayanan da gwamnatin kasar Amurka ta yi na cewa gwamnatin Buhari mai-ci ta na kokarin karkatar da kason kudin satar da aka dawo da su ga wasu tsirarrun mutane.

Jam’iyyar hamayyar ta ke cewa wadannan mutane da ake yunkurin ba wani kaso na dukiyar satar da aka maidowa kasar sun kunshi na kusa da fadar shugaban kasa da wani Gwamnan APC.

KU KARANTA: Kudin da Gwamnoni su ke samu daga asusun tarayya zai karu

Abacha: Kokarin dawowa Gwamnan Kebbi da $100m ya tonawa Buhari asiri – PDP
PDP ta zargi Shugaba Buhari da sake wawurar kudin satar Abacha
Asali: Facebook

Ologbondiyan a madadin PDP ya ke cewa an hana gwamnatin Buhari bada wasu daga cikin wannan kudi ga gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu, wanda shi ne shugaban gwamnonin APC.

“Maimakon karbo kudin da aka sace, gwamnatin tarayya ta na kokari ne na karkatar da Dala miliyan 100 (Naira biliyan 36.3) daga cikin kudin satar ga gwamna Bagudu.” Inji jam’iyyar.

Mai magana da yawun bakin na PDP, Mista Ologbondiya ya ke cewa wannan ya nuna irin mahaukaciyar sata, da yaudara da munufunci da ya cika gwamnatin shugaban kasa Buhari.

“Abin da Amurka ta fada ya tabbatar da magangunan da mu ka yi a baya na cewa gwamnatin Buhari ba ta da gaskiya, sannan ta zama inuwa ga marasa gaskiya.” Inji Kakakin PDP.

“Don haka mu ke kira Majalisa ta yi amfani da damarta, ta ceci martabatar kasar nan ta hanyar gudanar da cikakken bincike game da sha’anin karbar kudin satar da aka dawo da su.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel