Jerin Kujerun da APC Ta Lashe a Zaben Ranar 20 Yunin 2026
A ranar Asabar, 20 ga Yunin 2026 aka gudanar da zabe a Kano da wasu jihohin Najeriya shida, inda jam'iyyar APC ta lashe mafiya yawan kujerun.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - INEC ta ayyana waɗanda suka lashe zaɓukan cike gurbi na kujerun majalisar dattawa, majalisar wakilai ta tarayya da kuma majalisun dokokin jihohi da aka gudanar a jihohi daban-daban a ranar 20 ga Yunin 2026.
Jam’iyyar APC ta lashe kujeru 6 cikin 7, yayin da jam’iyyar PDP ta samu nasara a zaɓen cike gurbin kujerar Sanatan yankin Rivers ta Kudu maso Gabas.

Source: Facebook
A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku jerin kujerun da 'yan jam'iyyar APC ta samu a jihohin Najeriya aka gudanar da zaben.
Jerin kujerun da jam'iyyar APC ta samu
1. Gwamman jihar Ekiti
Jam’iyyar APC ta samu nasara a zaɓen gwamnan jihar Ekiti na shekarar 2026, inda aka ayyana gwamna mai ci, Biodun Oyebanji, a matsayin wanda ya lashe zaɓen da jimillar ƙuri’u 319,224.
Oyebanji ya yi nasara a dukkanin ƙananan hukumomi 16 na jihar, inda ya tattara kusan kashi 85 cikin 100 na sahihan ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen.
'Dan takarar jam’iyyar PDP, Wole Oluyede, ya zo na biyu da ƙuri’u 40,543, yayin da dan takarar ADC, Oluwadare Bejide, ya zo na uku da ƙuri’u 12,872.

Source: Facebook
2. Sanatan Enugu ta Arewa
A zaben da aka yi a mazabar Enugu ta Arewa, an ayyana Asogwa Ikeje Israel na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓ' cike gurbin.
The Guardian ta wallafa cewa sakamakon zaɓen ya kasance kamar haka:
- APC — ƙuri’u 162,360
- NDC — ƙuri’u 3,129
- ADC — ƙuri’u 1,676
- LP — ƙuri’u 1,027

Source: Facebook
3. Sanatan Nasarawa ta Arewa
Punch ta wallafa cewa Danladi Envulu-Anza na APC ya lashe zaɓen cike gurbin da aka gudanar domin maye gurbin marigayi Godiya Akwashiki.
Ga yadda sakamakon zaɓen ya kasance:
- APC (Danladi Envulu-Anza) — ƙuri’u 45,362
- LP (Labaran Maku) — ƙuri’u 12,931
- PDP (David Ombugadu) — ƙuri’u 11,570
- ADC (Alaku Ahmed) — ƙuri’u 4,244
- NDC (Duba Dodo) — ƙuri’u 1,496
- NNPP (John Araneshri) — ƙuri’u 102

Source: Facebook
4. Sanatan Ondo ta Kudu
Dayo Faduyile na jam'iyyar APC ya yi nasara a zaɓen cike gurbin da aka gudanar a ƙananan hukumomi shida na yankin Ondo ta Kudu.
The Cable ta wallafa cewa sakamakon zaɓen ya kasance kamar haka:
- APC (Dayo Faduyile) — ƙuri’u 68,474
- APM (Adeolu Akinwunmi) — ƙuri’u 1,411
- APP (Adesanya Olaoluwa) — ƙuri’u 213
- BP (Clement Funso-Nejo) — ƙuri’u 70

Source: Facebook
An gudanar da zaɓen ne domin cike gurbin da ya biyo bayan naɗa Jimoh Ibrahim a matsayin wakilin dindindin na Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya.
5. Majalisar Dawakin Kudu/Warawa
Legit Hausa ta rahoto cewa Rabiu Shuaibu na APC ya lashe zaɓen cike gurbin kujerar majalisar wakilai ta tarayya a mazabar Dawakin Kudu/Warawa a jihar Kano.
Ga sakamakon zaɓen:
- APC (Rabiu Shuaibu) — ƙuri’u 35,356
- APM (Lawal Haruna) — ƙuri’u 268
- LP (Abubakar Muhammad) — ƙuri’u 98

Source: Facebook
6. Majalisar Zuru
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta bayyana cewa Rabiu Aiki na APC ya lashe zaɓen cike gurbin kujerar majalisar dokokin jihar Kebbi.
Sakamakon zaɓen ya kasance kamar haka:
- APC (Rabiu Aiki) — ƙuri’u 4,871
- LP (Aliyu Muhammad) — ƙuri’u 168

Source: Facebook
PDP ta lashe zaben Rivers
A wani rahoton, mun kawo muku cewa Olaka Nwogu na jam’iyyar PDP ya lashe zaɓen cike gurbin kujerar sanata da aka yi a jihar Rivers.
Jami’ar tattara sakamakon zaɓen ta INEC, Rosemary Ogu ta sanar da sakamakon a ranar Lahadi cewa jam'iyyar APC ta yi nasara.
Dan takarar PDP da ya lashe zaben ya samu ƙuri’u 47,961 yayin da dan takarar jam'iyyar APC da ya biyo shi a baya, Osarosaka Ebenezer ya samu ƙuri’u 1,647.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


