Ministar Buhari ta yi bayanin gaskiyar dalilin da ya sa shugaban kasar ya yi afuwa ga tubabbun yan Boko Haram

Ministar Buhari ta yi bayanin gaskiyar dalilin da ya sa shugaban kasar ya yi afuwa ga tubabbun yan Boko Haram

- Sadiya Umar Farouq, Ministar harkokin agaji da hana annoba da kuma ci gaban al’umma, ta yi bayanin dalilin da yasa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi afuwa ga mayakan Boko Haram da suka tuba

- Ta ce dalilin yi wa tubabbun yan ta’addan afuwa ya kasance don basu damar sake tunani da ajiye ta’addanci domin suna iya taimakawa a bangarori daban-daban na ci gaban jama’a

- Ta yaba ma kokari da shirin Operation Safe Corridor, inda ta ce zai magance matsalolin rashin tsaro

Ministar harkokin agaji da hana annoba da kuma ci gaban al’umma, Sadiya Umar Farouq ta yi bayanin dalilin da yasa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi afuwa ga mayakan Boko Haram da suka tuba.

A cewarta, dalilin yi wa tubabbun yan ta’addan afuwa ya kasance don basu damar sake tunani da ajiye ta’addanci domin suna iya taimakawa a bangarori daban-daban na ci gaban jama’a.

Sadiya ta bayyana hakan ne lokacin da ta karbi bakuncin wakilan Shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Abayomi Gabriel Olonisaki, karkashin jagorancin jagoran Operation Safe Corridor, Manjo Janar Bamidele Shaffa, a Abuja.

Ministar Buhari ta yi bayanin gaskiyar dalilin da ya sa shugaban kasar ya yi afuwa ga tubabbun yan Boko Haram
Ministar Buhari ta yi bayanin gaskiyar dalilin da ya sa shugaban kasar ya yi afuwa ga tubabbun yan Boko Haram
Asali: UGC

A wani jawabi dauke da sa hannun mataimakiyar daraktan labarai, Rhoda Ishaku Iliya, ministar ta ce; “Don tabbatar da ganin cewa gwamnatin Buhari ta cimma nasara a kokarinta na magance matsalolin rashin tsaro da ta’addanci da ake ciki, gwamnatin tarayya ta bayar da wata dama da tubabbun yan Boko Haram Za su sake tunani da ajiye ta’addanci domin su taimaka a bangarori daban-daban na ci gaban jama’a.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Ramalan Yero ya fadi hanyar kawo zaman lafiya a Najeriya

“Ya kasance shiri mai matukar muhimmanci a ma’aikatar, daya daga cikin manufodin ma’aikatar shine mayar da hankali ga dawo da yankin arewa maso gabas, sabonta garuruwan da abun ya shafa da kuma tubabbun yan ta’addan Boko Haram.”

Ta yaba ma kokari da shirin Operation Safe Corridor, inda ta ce zai magance matsalolin rashin tsaro.

A wani labari na daban, mun ji cewa Yan ta'addan Boko Haram sun kona barikin yan sanda, cocina, gidan Janar Paul Tarfa da gidajen mutane a mumunan harin da suka kai jihar Adamawa ranar Juma'a, 21 ga watan Febrairu, 2020.

Majiya daga garin Gargisa, ya bayyana yadda yan ta'addan suka sace dukayar al'umma kafin bankawa gidajen wuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel