Tallar Kosai da Karago: ’Yan Najeriya Sun Dura kan Matar Tinubu bayan Kalamanta
- An dura kan uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, bayan ta bukaci ‘yan Najeriya su fara kananan sana’o’i kamar kosai da gasasshen masara
- Ta bayyana cewa shirin Renewed Hope Initiative na bayar da tallafi ne ba rance ba, domin taimaka wa masu karamin karfi su fara sana’o’i
- Wasu sun soki kalaman nata suna cewa ba su dace da halin kuncin rayuwa ba, yayin da wasu suka kare sana’o’in a matsayin halal kuma masu riba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta fuskanci suka daga wasu ‘yan Najeriya bayan ta ba da shawarar fara kananan sana’o’i.
Sanata Oluremi Tinubu ta ba da shawarar fara sayar da kosai, gasasshen masara da karago domin samun abin dogaro.

Source: Twitter
Remi Tinubu ta yi wannan bayani ne yayin da take magana da wakilan fadar shugaban kasa bayan taron kwata na biyu na shirin Renewed Hope Initiative, kamar yadda Arise TV ta yada bidiyon a Youtube.
Shawarar da matar Bola Tinubu ta bayar
A cewarta, shirin na ci gaba da taimaka wa marasa galihu ta hanyar bayar da tallafi kai tsaye maimakon rance domin su samu damar kafa sana’o’insu.
Ta ce fara sana’ar kosai ko gasasshiyar masara ba ta bukatar jari mai yawa, kuma gwamnati ta yi kokarin karfafa gwiwar jama’a ta hanyar ba su tallafin da zai taimaka musu.
Uwargidan shugaban kasar ta kuma bayyana cewa shirin ya tallafa wa bangarorin lafiya, noma, ilimi da saka hannun jari na zamantakewa domin inganta rayuwar al’umma.

Source: Facebook
Gudunmawar da Oluremi Tinubu ke bayarwa
A cewarta, ta bayar da Naira biliyan biyu domin yaki da cutar tarin fuka, biliyan daya domin kula da masu fama da cutar sankarar mama, da kuma Naira miliyan 500 don magance matsalar karancin abinci mai gina jiki.
Haka kuma ta ce an samar da guraben karatu, horas da matasa kan fasahar sadarwa da kuma tallafawa shirye-shiryen noma da sauran ayyukan raya kasa.
Ta bukaci ‘yan Najeriya ka da su yanke kauna duk da matsin tattalin arzikin da ake fuskanta, tana mai cewa manufar Renewed Hope Agenda ita ce sabunta fata da kwarin gwiwa.
Martanin wasu yan Najeriya kan kalaman Oluremi
Sai dai kalaman nata sun jawo martani a kafafen sada zumunta, inda wasu suka zarge ta da rashin fahimtar irin wahalhalun tattalin arzikin da talakawa ke ciki a halin yanzu.
Wasu yan Najeriya da ke amfani da kafafen sada zumunta sun kare ta, suna cewa sana’o’in kosai, gasasshiyar masara da kuli-kuli sana’o’i ne na gaskiya da ke samar da riba ga masu gudanar da su.
@firstladyship da ta saba adawa da mulkin APC ta ce:
"’Yan Najeriya suna cikin mawuyacin hali. Matsaloli sun yi kamari, amma mutane sun gaji da kokarin guje musu."
@ireteeh:
“Uwargidan Shugaban Kasa tana tallafa wa mutane da sana’o’in kosai, masara da kuli-kuli, alhali wani talaka na horas da mutane domin gina ingantattun sana’o’i a fannin tsaron yanar gizo.”
@Akikanju1568901 ya ce:
“Masu sayar da kosai sun taimaka wa yara da dama su shiga jami’o’i, sun gina gidaje, kuma sun sayi motoci.”

Kara karanta wannan
'An yi masa karya': Hadimin Tinubu ya kare shi kan alkawarin gyara wutar lantarki
Oluremi Tinubu ta kunyata gwamna a bainar jama'a
An ji cewa Gwamna Ademola Adeleke ya gamu da cikas daga wurin uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu a taron cikar Ooni na Ife shekara 10 a gadon mulki.
Lamarin ya faru ne lokacin da Gwamna Adeleke ke gabatar da jawabinsa, inda aka ga yana rawa a wurin taron wanda ya gudana.
A faifan bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta, an ga yadda matar Tinubu ta taka wa Gwamna Adeleke burki saboda kurewar lokaci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

