Yadda gwamnan Bauchi ya baiwa kamfaninsa kwangilan bilyan N3.6bn yana

Yadda gwamnan Bauchi ya baiwa kamfaninsa kwangilan bilyan N3.6bn yana

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya baiwa kamfanin da shi ne diraktanta kwangilan kudi sama da bilyan uku da rabi , kuma hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa ga masu rike da mukaman mulki, Premium Times ta ruwaito.

Kwangilar ita ce sayan motoci 105 domin amfanin gwamnan da wasu jami'an gwamnatin jihar.

Kuma duk da hakan, ana cece-kucen cewa kamfanin bata wanzar da kwangilan kamar da aka bukata ba.

Jami'an da suka san lamarin kwangilan sun bayyana cewa kamfanin Adda Nigeria Limited, aka baiwa kwangilan kuma gwamnan jihar Bauchi na da hannun jarin kashi 20 cikin 100 a kamfanin.

Gwamnan wanda tsohon minista birnin tarayya ne ya lashe zaben jihar ne saboda kukan mutan jihar Bauchi kan magabacinsa, Mohammed Abubakar.

Gabanin zamansa gwamna, Bala Mohammed na gurfanar gaban kotu kan tuhumar almundahanan kudade lokacin da yake minista.

Hukumar EFCC ta shigar da shi kotu kan zargi-zargi shida na almundahana da babakekere. Amma ya musanta dukkan zargin.

A watan Afrilu 2019, bayan nasara a zaben gwamnan jihar Bauchi, hukumar EFCC ta sake daura masa wasu laifuka a babbar kotun birnin taraya kan zargin amsan cin hancin N500 million.

Hakazalika an tuhumesa da laifin rashin bayyana wasu dukiyoyinsa.

KU KARANTA: Yan Boko Haram sun sun kona barikin yan sanda, Coci da gidan Janar a Adamawa

A bangare guda, Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Sani Yariman Bakura, ya bayyana cewa zai fito takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023 a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.

Ahmed Sani Yariman Bakura ya ke cewa duk da shi ‘Dan Arewa ne zai tsaya takarar shugaban kasa, tun da shi ‘Dan Najeriya ne domin bai yadda da siyasar bangaranci ba.

Sanata Ahmad Yariman Bakura wanda ya yi aikin gwamnati, ya kuma yi gwamna daga 1999 zuwa 2007, kafin ya zama Sanata, ya ce kowa ya na da damar ya mulki Najeriya.

A hirarsa da ya yi wa Daily Trust da ta fito a Ranar Lahadi, ya ce: “Mutane sun fara samu na domin yi mani kamfen din shugaban kasa. Jama’a su na roko na in fito takara. a 2023”

A cewarsa, Muhammadu Buhari ba zai mikawa Asiwaju Bola Tinubu ragamar APC ba, inda ya ce ko da akwai wata yarjejeniya a tsakaninsu, ba za ta yi aiki a zabe mai zuwa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://twitter.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel