Yan Boko Haram sun sun kona barikin yan sanda, Coci da gidan Janar a Adamawa

Yan Boko Haram sun sun kona barikin yan sanda, Coci da gidan Janar a Adamawa

Yan ta'addan Boko Haram sun kona barikin yan sanda, cocina, gidan Janar Paul Tarfa da gidajen mutane a mumunan harin da suka kai jihar Adamawa ranar Juma'a, 21 ga watan Febrairu, 2020.

Majiya daga garin Gargisa, ya bayyana yadda yan ta'addan suka sace dukayar al'umma kafin bankawa gidajen wuta.

Yace: "Sun shigo da yawa, tare da motoci 14 suka dira garin; kuma suka sace shagunan sayar da magani da kayan abinci."

"Sun samu damar cin karansu ba babbaka saboda an janye bataliyan Sojin da ke garin kwanakin baya kuma aka bar wasu yan tsirarun Soji da suka gaza kawar da yan ta'addan."

"Bayan sace-sacen da sukayi, sun kona barikin yan sandan, cocina biyu na Living Faith da EYN, da kuma kantin kaya."

"Hakazalika an kashe mutane amma ban san adadinsu ba a yanzu."

"Kana sun kona gidan Janar Paul Tarfa, tare da gidaje masu muhimmanci a garin."

Yan Boko Haram sun sun kona barikin yan sanda, Coci da gidan Janar a Adamawa
Yan Boko Haram sun sun kona barikin yan sanda, Coci da gidan Janar a Adamawa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda gwamnan Bauchi ya baiwa kamfaninsa kwangilan bilyan N3.6bn yana

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Suleiman Nguroje, ya ki tsokaci kan lamarin saboda harkar Sojoji ne.

A bangare harin da 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram suka kai a wani sashi na jihar Adamawa a baya-bayan nan ya janyo hankalin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abukakar.

Atiku ya ce, "Hare-haren da Boko Haram ke kai wa ga rayuka da dukiyoyin'yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba ya kai wani mataki mai ban tsoro.

"Ina yi wa mutanen jiha ta na garin Garkidi addu'a a kan harin da ya faru a cikin karshen mako. Ina fata Allah ya bawa iyalansu hakurin jure rashin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel