Yanzun-nan: An tabbatar da mutuwar hazikin soja daya a harin da Boko Haram ta kai Garkida

Yanzun-nan: An tabbatar da mutuwar hazikin soja daya a harin da Boko Haram ta kai Garkida

Rundunar sojin Brigade 23 ta tabbatar da cewar soja daya ya mutu yayinda wani ya jikkata a lokacin da rundunar ya yi arangama da yan ta’addan Boko Haram wadanda suka kai hari Garkida a ranar Juma’a.

Majiyarmu ta ce ta samu jawabi daga rundunar a safiyar yau Lahadi, 23 ga watan fabrairu game da barnar na Garkida.

Boko Haram sun kai mamaya garin Garkida da ke arewacin Adamawa a karamar hukumar Gombi da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar Juma’a Sannan suka lalata gidaje, cocina, shaguna da ababen hawa.

A jawabinta, rundunar Bridade 23 wacce ke da hedkwatar ta a Yola, ta bayyana cewa ba don dakarunta sun dauki matakin dakile yan ta’addan da kashe wasun su ba, da barnar ya fi haka.

Sai dai ta ce sun rasa wani soja a arangaman.

Yanzun-nan: An tabbatar da mutuwar hazikin soja daya a harin da Boko Haram ta kai Garkida
Yanzun-nan: An tabbatar da mutuwar hazikin soja daya a harin da Boko Haram ta kai Garkida
Asali: UGC

A wani jawabi dauke da sa hannun Manjo Haruna Mohammed Sani, mataimakin daraktan labarai na rundunar Brigade 23 ya ce, “dakarun Bataliya ta 232 na Brigade 23 karkashin Operation Lafiya Dole da aka tura Garkida, karamar hukumar Gombi a jahar Adamawa t dakile wani shirin kai harin ta’addanci da yan ta’addan Boko Haram suka so yi a garin mai cike da zaman lafiya a ranar 21 ga watan Fabrairu.

“Yan ta’addan sun kai farmaki garin cikin kimanin manyan motocin bindiga guda bakwai da wasu babura, inda suka cinna wa wasu gine-gine wuta da haddasa tashin hankali a garin.

“Sai dai dakarun sojin da aka zuba sun sha kan yan ta’addan inda suka yi musayar wuta wanda ya yi sanadiyar halaka yan ta’adda da dama sannan sauran suka tsere da raunuka.

KU KARANTA KUMA: Ministar Buhari ta yi bayanin gaskiyar dalilin da ya sa shugaban kasar ya yi afuwa ga tubabbun yan Boko Haram

“Abun bakin ciki, hazikin soja daya ya mutu sannan wani ya jikkata a arangaman. Tuni aka kwashi wanda ya jikkata zuwa asibitin sojoji kuma yana samun sauki.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel