Buhari ya bayyana sharudan bude iyakokin Najeriya

Buhari ya bayyana sharudan bude iyakokin Najeriya

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya gindaya sharadin bude iyakokin kasar domin barin kaya su shigo daga kasashe da ke makwabtaka.

Buhari ya bayyana cewa bude iyakokin kasar ya dogara ne a kan rahoton kwamitin bangare uku da ya hada da gwamnatocin Najeriya, na jamhuriyar Benin dana jamhuriyar Nijar.

Shugaban kasar ya sanar da hakan ne a lokacin da ya hadu da Shugaba Roch Marc Christian Kabore na kasar Burkina Faso, wanda ya kai masa ziyara a ranar Juma’a a gidan gwamnati da ke Abuja, Channels TV ta ruwaito.

Buhari ya bayyana sharudan bude iyakokin Najeriya
Buhari ya bayyana sharudan bude iyakokin Najeriya
Asali: Twitter

Kakakin Shugaban kasar Mallam Garba Shehu ya ce: “Babbar matsalarmu shine tsaro, shigo da makamai, harsasai da kuma kwayoyi.”

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya kara da cewa, “mun fahimci raguwa a ta’addanci tun bayan da muka rufe iyakokin kasarmu. Hakazalika, manonanmu yanzu na iya siyar da shinkafar gida tunda mun daina shigo da ta waje wacce ke cika kasar nan. Zan yi aiki da gaggawa matukar na samu rahoto.”

Shugaban Burkina Faso wanda shine shugaban kwamitin ECOWAS wanda hakkin shawo kan matsalar rufe iyakoki ya rataya wuyansu, ya sanar da Buhari cewa ya zo ziyarar ne don sauke hakkin ECOWAS da ke kansa.

KU KARANTA KUMA: Ministar Buhari ta yi bayanin gaskiyar dalilin da ya sa shugaban kasar ya yi afuwa ga tubabbun yan Boko Haram

Shugaban kasa Kabore ya ce, akwai kalubale da yawa wadanda suka sa Najeriya ta garkame iyakokinta Buhari ya sanar masa. Yayi kira ga Shugaban kasa Buhari da ya kara duba matsayarsa.

A wani labarin kuma, mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero, ya yi magana a game da halin rashin tsaro da ake fama da shi a Najeriya inda ya bada wasu shawarwari.

Mukhtar Ramalan Yero ya ke cewa abubuwa biyu ne su ka jefa kasar a halin da ta ke ciki. A na sa ra’ayin ba komai ba ne wadannan sai talauci da rashin shugabanci.

Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya nuna cewa muddin ba a fito an yi yaki da talauci da kuma bata-garin shugabanni ba, ba za a taba samun zaman lafiya a Najeriya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel