Latest
Jami'an rundunar 'yan sanda sun kashe yan daba takwas tare da dakile wani yunkurin kai hari Hedikwatarsu ta Orlu a jihar Imo a ranar Alhamis, 6 ga watan Mayu.
Masanin tattalin arzikin kasa Pat Utomi ya bayyana hasashensa kan irin yanayin da Najeriya kan iya idan ba a zauna an magance halin da ake ciki na tsaro ba.
Mazauna babban birnin tarayyar kasar, na cikn halin fargaba kan jita-jitar 'yan fashi da ke tarewa a wajen Abuja, tuni wasu suka janye yaransu daga makarantu.
Sanata mai wakiltar Osun ta gabas, Francis Fadahunsi, yayi kira ga majalisar dattawa da ta dauka mummunan mataki domin kawo karshen kalubalen tsaro da ya dame.
Za ku ji cewa Marasa galihu da ‘Yan IDP samu abin buda baki daga wajen Bola Tinubu. Tinubu ya raba buhunan kayan abinci domin Musulmai su samu abin buda-baki.
Ganin ana takun saka a Jam’iyyar PDP na reshen Jihar Kuros Riba, Kungiyar Gwamnonin PDP ta ziyarci Ben Ayade domin a hana shi sauya-sheka zuwa jam'iyyar APC.
Biyo bayan dakatar da Manajan Daraktar hukumar kula jiragen ruwan Najeriya, gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti don gudanar wani bincike a hukumar cikin gaggawa.
A jihar Legas, gobara ta yi kaca-kaca da kasuwar sayar da kayyakin atamfa. An ruwaito cewa, hukumar kashe gobara ta jihar ta kama hanya don zuwa kashe wutar.
A wata jiha kuwa, an ruwaito cewa, 'yan bindiga sun tare wata motar banki mai dauke makudan kudade, in da suka suka yi awon gaba da wasu adadi da ba a sani ba.
Masu zafi
Samu kari