Allah ya yiwa Sarkin Malaman Fika rasuwa, Gwamna Buni ya yi ta'aziyya
- Sarkin Malaman masarautar Fika a jihar Yobe ya rigamu gidan gaskiya
- Gwamnan Yobe ya aike da sakon ta'aziyyarsa
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, a ranar Juma'a ya aika sakon ta'aziyya ga Mai martaba Sarkin Fika, Muhammadu Abbali Ibn Muhammadu Idrisa, sakon ta'aziyyar rashin Sarkin Malaman Masarautar, Imam Muhammad Alkali.
Limamin ya mutu ne a asibitin koyarwan jami'ar Maiduguri inda yayi jinyar rashin lafiya.
Gwamna Buni ya ce Limanin Fika ya rasu lokacin da al'ummar Masarautar suka fi bukatarsa.
Sakon ta'aziyyarsa na kunshe cikin jawabin da Dirakta Janar na harkokin labaran gwamnan, Kwamred Mohammed Mamman, ya saki, rahoton Vanguard.
Gwamnan yace, "Imam Muhammad Alkali ya mutu a lokacin da ake bukatarsa ya janyo hankalin mabiyansa su yiwa jihar kasa addu'a a wannan lokaci mai tsanani."
KU KARANTA: Jerin kasashe 20 mafi shugabannin kwarai a duniya, Rahoton Bincike
KU DUBA: Haramun Ne Yin Kasuwancin Bitcoin, in Ji Shehin Malami Daga Kano
A wani labarin daban, fasinjoji 14, ciki har da yara uku, sun kone kurmus a wani hadari da ya faru a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hadarin wanda ya faru da misalin karfe 10:20 na daren ranar Alhamis ya cika da wata mota kirar Toyota RAV 4 kalar azurfa mai lamba, LND 13 GS; motar Toyota Camry mai lamba, GGE 369 GJ da kuma wata motar bas kirar Mazda da ba a san lambarta ba.
An tattaro cewa wata motar bas ta kasuwa da ta sha gaban wata mota ba bisa ka'ida ba ta bugi wata batacciyar mota kirar Toyota Rav 4 da aka ajiye a tsakiyar hanya.
Asali: Legit.ng