Da Duminsa: Rikici Ya Ɓarke Tsakanin Ƴan Sanda da Ƴan Acaɓa a Legas
- An yi arangama tsakanin jami'an yan sanda da yan acaba a unguwa Ogba a Legas
- Hakan ya biyo bayan harbin wani dan acaba da jami'in dan sanda ya yi ne a yankin
- Wata majiya ta ce dan sandan ya harbi dan acaban ne saboda ya dauke shi bai kuma biya shi kudinsa ba
An shiga zaman ɗar-ɗar a unguwar Ogba, jihar Legas kan zargin harbe wani ɗan acaɓa da wani ɗan sanda ya yi.
Wata majiya ta shaidawa The Punch cewa rikicin ya fara ne tun jiya a lokacin da ɗan sandan ya ƙi biyan ɗan acaɓan kudin ɗaukansa da ya yi.
DUBA WANNAN: Mutanen Gari Sun Ƙona Ƴan Bindiga Uku Ciki Har da Mace a Sokoto
Wata majiya da ta nemi a ɓoye sunanta ta shaidawa majiyar Legit.ng cewa an kashe mutum biyu a daren jiya Alhamis.
"Faɗa ne tsakanin ƴan sanda da ƴan acaɓa. Ɗan acaɓa ya ɗauki ɗan sanda zuwa wani wuri a jiya, sai ya tambayi kuɗin aikinsa daga hannun ɗan sandan bayan ya sauke shi. Ɗan sandan ya ƙi biyan shi kuɗin sannan ya harbe shi.
KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Jarida, Sunyi Garkuwa da Matafiya da Dama a Katsina
"An ji ƙarar harbe-harbe a yau da safe. Mintuna ƙalilan da suka shuɗe. Dukkan ƴan acaɓa sun sauka daga baburansu suna shirin yin zanga-zanga," a cewar majiyar.
A yayin hada wannan rahoton, rundunar yan sandan jihar ta girke yan sandan kwantar da tarzoma da kuma jami'an farin kaya don tabbatar da doka da oda.
Daily Trust ta ruwaito cewa an girke manyan motoci cike da jami'an tsaro don samar da nutsuwa a yankin.
Tuni aka kulle hanyoyin da za su kai shataletalen Excellence, kasuwar Ogba da kuma WAEC da motocin jami'an (RRS) na rundunar yan sanda.
Duka shagunan kasuwar a kulle suke lokacin da wakilin majiyar mu ya kai ziyara.
A lokacin hada wannan rahoton, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Legas, CSP Muyiwa Adejobi baya amsa wayarsa sannan bai amsa sakonnin kar ta kwana da aka aika masa ba.
A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.
Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.
Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.
Asali: Legit.ng