Jita-Jitan Hare-Haren Yan Bindiga Ya Kawo Hargitsi a Abuja Yayin da Iyaye Ke Janye Yara Daga Makarantu

Jita-Jitan Hare-Haren Yan Bindiga Ya Kawo Hargitsi a Abuja Yayin da Iyaye Ke Janye Yara Daga Makarantu

- Yayin da matsalar rashin tsaro ta bazu a fadin jihohi, ana cikin wani yanayi na fargaba a babban birnin tarayyar kasar, Abuja

- Rahotannin sun ce tuni wasu iyayen suka fara janye yaransu daga makarantun da ke wajen garin saboda tsoron satar mutane

- Gwamnan jihar Neja a kwanan baya ya bayyana cewa tafiyar awa biyu ne kadai tsakanin ‘yan kungiyar Boko Haram da Abuja

Wani rahoto na jaridar The Guardian ya nuna cewa akwai fargaba a Abuja kan jita-jitar 'yan fashi da ke tarewa a wajen babban birnin Najeriyar.

Babban birnin tarayya, FCT na kewaye da jihohi wadanda suka fuskanci hare-hare daga yan fashi da yan ta’adda a yankin su.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan gudun hijira na taimaka wa ‘yan ta’addan Boko Haram wurin kai hari a Ajiri

Jita-Jitan Hare-Haren Yan Bindiga Ya Kawo Hargitsi a Abuja Yayin da Iyaye Ke Janye Yara Daga Makarantu
Jita-Jitan Hare-Haren Yan Bindiga Ya Kawo Hargitsi a Abuja Yayin da Iyaye Ke Janye Yara Daga Makarantu Hoto: @abusbello
Asali: Twitter

A cikin jihar Neja da ke kusa, an yi garkuwa da mutane da dama kwanakin da suka gabata daga garin Shadadi da ke karamar hukumar Mariga kusa da babban birnin Najeriya.

A cewar wani mazaunin yankin, sama da ‘yan bindiga 1,000 ne suka kai hari yankin, inda suka kashe mutane takwas tare da raunata hudu, yayin da duk wadanda suka tsira suka tsere.

Kwamishinan yada labarai na jihar Neja, Sani Idris, ya tabbatar da afkuwar harin sannan ya ce a yanzu haka suna kan tattara alkaluman mutanen da harin ya shafa.

Tuni, iyaye a Abuja, musamman a Karamar Hukumar Bwari, suka fara janye yaransu gaba daya daga makarantu kan wasu daruruwan mutane da ake zargin mayakan Fulani ne a Sabon-Wuse, wani garin kan iyaka da jihar Neja.

A cewar rahotanni, wadanda ake zargin mayakan Fulani ne da suka badda kamanni a matsayin makiyaya sun tsallaka babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna kusa da garin Sabon-Wuse a Neja a ranar Laraba, 5 ga watan Mayu lamarin da ya haifar da tashin hankali yayin da mazauna yankin suka firgita suna zaton hari ne.

Da yake martani a kan ci gaban, Ministan Babban Birnin Tarayya, Malam Muhammad Bello, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da yin aiki tare da Sojojin Najeriya da duk sauran hukumomin tsaro don ci gaba da kare birnin na FCT.

A cewar jaridar Leadership, Ministan ya bayar da tabbacin ne lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga Hedikwatar Tsaro da ke Abuja.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Bindiga Sun Afkawa Motar Kudi, Sun Kwashi Makudan Kudade

Bello ya ce Abuja ta kasance cikin kwanciyar hankali saboda dangantakar aiki da ke tsakanin shugabannin rundunonin sojoji daban-daban da sauran hukumomin tsaro a babban birnin tarayya a tsawon shekaru.

A wani labarin kuma, Sheikh Ahmad Gumi ya ce yan bindigan da sukayi garkuwa da daliban jami'ar Greenfield a Kaduna sun fasa kashesu kamar yadda sukayi barazana ranar Litinin.

Za ku tuna cewa a ranar Litnin, shugaban yan bindigan ya ce idan ba'a biya N100m ba zasu kashe daliban ranar Talata.

Amma a ranar Alhamis yayin karban bakuncin iyayen daliban Afaka da aka ceto jiya, Malamin addinin ya ce yanzu haka suna tattaunawa don ceto daliban jami'ar Greenfield.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng