An Bankaɗo Girman Ɓarnar da Iran Ta Yi wa Amurka, abin Ya Wuce Yadda Ake Faɗa
- Akalla gine-gine da kayan yaƙi 228 na Amurka ne Iran ta lalata ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa da makami mai linzami tun farkon wannan yaƙin
- Hotunan tauraron ɗan adam sun nuna cewa barnar ta haura abin da gwamnatin Amurka ta fada a baya, inda aka lalata rumbunan mai, radar, da jiragen yaƙi
- Rufe mashigar ruwa ta Hormuz da Iran ta yi ya haddasa babban koma-baya ga tattalin arzikin duniya, inda ake rasa gangar mai miliyan 10 a kowace rana
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - A ranar 28 ga Fabrairu, 2026, yaki ya barke a Gabas ta Tsakiya tsakanin Amurka, Isra'ila da kuma Iran, rikicin da ya sauya tattalin arzikin duniya.
Hare-haren sararin samaniya na Iran, waɗanda akasari aka kai su ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa, sun lalata ko ruguza akalla gine-ginen tsaro ko kayan aiki 228 a sansanonin sojan Amurka.

Kara karanta wannan
Bayan abin da ya faru, an haramta wa masu digirin girmamawa amfani da 'Dr' a Najeriya

Source: Getty Images
Binciken barnar da Iran ta yi wa Amurka
Binciken da Washington Post ta gudanar ya bayyana cewa waɗannan hare-haren sun shafi rumbunan ajiye jiragen sama, dakunan kwanan sojoji, rumbunan mai, da kuma muhimman kayan aikin radar da sadarwa na kariya.
Hotunan tauraron ɗan adam sun nuna cewa girman barnar da Iran ta yi wa kadarorin Amurka a Gabas ta Tsakiya ya fi yadda aka bayar da rahoto a baya.
Hare-haren na Iran sun yi sanadin mutuwar sojojin Amurka bakwai, shida a Kuwait sannan ɗaya a Saudiyya, yayin da wasu sojoji sama da 400 suka samu raunuka daban-daban.
Iran ta kai waɗannan hare-hare ne a matsayin martani ga harin hadin gwiwa na Amurka da Isra'ila a ƙasarta, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 3,500.
Asarar jiragen da Amurka ta yi
A ranar Talata, wani jirgin sama na rundunar sojan sama ta Amurka nau'in KC-135 Stratotanker, wanda darajarsa ta kai dala miliyan 40 zuwa 52, ya ɓace a sararin samaniyar mashigar Hormuz.
Kodayake Times of India ta ruwaito cewa gidajen watsa labaran Iran sun bayar da rahoton bacewar jirgin, babu wata sanarwa daga Tehran da ke nuna cewa tana da hannu a ciki.
Rahotannin sirri na rukunin fasahar tsaro na TWZ sun nuna cewa, Amurka ta yi asarar jiragen yaƙi 39, ciki har da jirage huɗu nau'in F15E Strike Eagle a makon farko na Afrilu.
Amurka ta rasa wasu jirage guda 10 da suka samu matsala daban-daban sakamakon hare-haren Iran, yayin da Daular Larabawa ta ce Iran ta kai hare-hare a kasarta na kwanaki biyu a jere, har ma wani harin ya janyo gobara a matatar mai da ke Fujairah.
Hare-haren Iran a kasashen Gulf
Iran ta kai hare-hare a wurare da dama a fadin Gabas ta Tsakiya a matsayin martani ga harin da Amurka da Isra'ila suka kai mata. Hare-haren sun fi mayar da hankali ne kan kadarorin Amurka da ke kasashen Gulf.
Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta bayyana cewa Iran ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka a cikin kasarta har na tsawon kwanaki biyu a jere.
Daya daga cikin wadannan hare-haren, kamar yadda mahukuntan Abu Dhabi suka bayyana, ya haddasa gobara a wata matatar mai da ke Fujairah, inda aka samu raunukan wasu 'yan kasar Indiya su uku.

Source: Getty Images
Rikicin mashigar Hormuz da matakin Trump
Legit Hausa ta ruwaito cewa Iran ta rufe mashigar ruwa ta Hormuz, wadda ita ce hanyar da kusan kashi ɗaya bisa biyar na danyen mai da iskar gas (LNG) na duniya ke bi ta cikinta.
Wannan rufewar ta haifar da babbar asara a tarihin samar da makamashi, inda Hukumar Makamashi ta Duniya, IEA ta bayyana cewa an rasa gangar mai miliyan 10 a kowace rana tare da rage samar da iskar gas da kashi 20 a duniya.
Domin kawo karshen wannan matsala, rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta ƙaddamar da aikin "Project Freedom" a ranar Litinin don raka jiragen ruwa ta mashigar Hormuz, tare da tallafin jiragen sama 100 da jami'ai 15,000.
To sai dai, bayan kwana ɗaya kacal a ranar Talata, Shugaba Donald Trump ya sanar da dakatar da wannan aikin soja da nufin cimma yarjejeniya da Iran don kawo ƙarshen yaƙin, kamar yadda muka ruwaito.

Kara karanta wannan
Iran ta yi magana, da yiwuwar yaki ya kuma barkewa tsakanin kasar Musulunci da Amurka
Hormuz: Amurka ta farmaki jiragen Iran
A wani labari, mun ruwaito cewa, sojojin kasar Amurka sun kai hari kan wasu jiragen ruwa da suka nufi Iran a kusa da mashigar Hormuz
Gwamnatin Iran ta tabbatar da kai harin, inda ta ce an kashe wasu daga cikin fararen hula da ke cikin jirgin ba tare da sun aikata laifi ba.
Hakan na zuwa ne yayin da lamura ke kara zafi tsakanin Amurka da Iran a Gabas ta Tsakiya, musamman kan mashigar ruwan Hormuz.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

