Wata Sabuwa: Japan da Amurka Sun Harba Makamai, Sun Fusata China

Wata Sabuwa: Japan da Amurka Sun Harba Makamai, Sun Fusata China

  • Japan ta hada kai da kasar Amurka ta harba makamai masu linzami tare da nutsar da wani jirgin yaki a wani atisaye da ta ke a kusa Philippines da Taiwan
  • Biyo bayan lamarin, China ta yi Allah wadai da atisayen, tana zargin Japan da kara komawa tsarin karfin soja duk da abubuwan da suka faru a baya
  • Rahoto ya nuna cewa atisayen da aka yi ya hada sojoji kusan 17,000 a shirin da Japan ke yi na kara karfafa tsaronta ta hanyar hadin gwiwa da kasashe

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

China - Japan ta harba makamai masu linzami kan wani jirgin ruwa tare da nutsar da wani tsohon jirgin yaki a ruwa tsakanin Philippines da Taiwan.

An bayyana cewa ta yi haka ne a wani bangare na manyan atisayen soja da suka hada da sojojin Amurka, lamarin da ya fusata China.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Amurka ta nemi taimakon majalisar dinkin duniya kan batun Iran

Sojojin Japan a bakin aiki
Yadda sojojin Japan ke atisaye. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

AFP. ta wallafa cewa Firaministar Japan, Sanae Takaichi, ta kara saurin sauya salon tsaron kasar zuwa matakai masu zafi, tana nisantar da Japan daga tsarin kin yaki da ta runguma a baya tare da goyon bayan Amurka.

Makaman da Japan ta harba

Harba makamai masu linzami guda biyu kirar Type-88 wani bangare ne na atisayen da ake gudanarwa a Philippines tsakanin sojojin Amurka, Australia, Philippines da Japan, tare da rundunoni daga Faransa, New Zealand da Canada.

Ministocin tsaron Japan da Philippines sun halarci kallon harba makaman a lardin Ilocos Norte da ke Arewacin kasar, mai tazarar kusan kilomita 400 daga Taiwan.

Jami’ai sun ce makaman guda biyu sun bugi wani tsohon jirgin ruwan yaki na rundunar ruwa ta Philippines, mai nisan kusan kilomita 75 daga gabar teku a Tekun Kudancin China, lamarin da ya sa jirgin ya nutse.

A shekarun baya-bayan nan, Japan ta fara neman samun damar kai farmakin ramuwar gayya tare da kara kasafin kudin soja da kuma zurfafa hadin gwiwar tsaro da kawayenta a yankin ciki har da Philippines.

Kara karanta wannan

Yaki na shirin dawowa: An zargi Iran ta harba makamai masu linzami UAE

Makamin da Japan ta harba
Wani makami da sojojin Japan suka harba yayin atisaye. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Harba makaman ya fusata China

RFI ta wallafa cewa dangantakar China da Japan da ta dade tana samun koma baya kuma ta kara tabarbarewa bayan zuwan Firaminista Takaichi.

Ana kallon Takaichi mai ra’ayin rikau kuma mai tsauraran manufofin tsaro, ta bayyana a baya cewa Japan na iya shiga yaki idan China ta yi yunkurin kwace Taiwan.

A ranar Laraba, Beijing ta sake yin Allah wadai da gwajin makaman, tana mai cewa:

“Wani sabon misali ne na yadda masu ra’ayin rikau a Japan ke kokarin kara maida kasar ta zama mai karfin soja.”

Amurka ta nemi hafin kan China

A wani labarin, kun ji cewa Amurka ta sake gabatar da wani kudiri a gaban majalisar dinkin duniya game da amfani da karfi wajen bude Hormuz.

Mininistan harkokin wajen Amurka, Macro Rubio ya yi kira ga kasashen China da Rasha da suke da kujerar naki a majalisar da su goyi bayan kudirin.

A kwanakin baya ma dai Amurka ta gabatar da irin kudirin amma kasashen China da Rasha suka hau kujerar naki wajen fatali da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng