Batancin ga Annabi: Duk da shigar 'yan sanda, ana cigaba da rikici a Legas
- Ko bayan da 'yan sanda suka kama mutum 45 a kan zargin tada tarzoma a Mile 12 dake Legas, rikicin bai tsaya ba
- Duk da kwamishinan 'yan sandan jihar, Hakeem Odumosu, ya bada umarnin cafke mutum 13, kungiyoyin yankin basu dena kai farmaki ba
- An gano cewa ko a ranar Alhamis, 'yan daban sun cigaba da kai farmaki yankin a kan zargin batancin da aka yi wa Annabi Muhammad
Duk da shigar 'yan sanda tashin hankalin dake faruwa a yankin Mile 12 a jihar Legas, kungiyoyin dake fada sun cigaba da tada zaune tsaye.
Premium Times ta ruwaito yadda 'yan sanda suka cafke mutum 45 da ake zargi bayan rikicin ya barke a yankin Mile 12.
'Yan sandan sun ce lamarin ya faru ne bayan zargin wani Alhaji Alidu da aka yi da batanci ga Annabi Muhammad. Shine kwamandan kungiyar 'yan sintirin yankin Gengere.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Hakeem Odumosu, ya bada umarnin damke shugabannin kungiyoyi 13 dake cigaba da tada zaune tsaye a yankin.
KU KARANTA: Tantance 'yan takarar LG na APC: Mai digirin digirgir ya koka kan hana shi takara
KU KARANTA: Boko Haram: 'Yan majalisar dattawa sun gigice bayan sanarwar za a kai farmaki
A yayin da jami'an 'yan sanda suke kokarin shawo kan hargitsin Mile 12, 'yan daban sun cigaba da kaddamar da hare-hare a yankin.
Sabbin hare-haren sun auku ne a ranar Alhamis kuma ya bar mazauna yankin, 'yan kasuwa da masu wucewa cikin tashin hankali.
Har yanzu ba a tabbatar da cewa ana hare-haren bane saboda zargin batancin da aka yi wa Annabi Muhammad.
A wani labari na daban, kasa da sa'o'i 24 da nada sabon kwamishinan 'yan sanda a jihar Anambra, Christopher Adetokumbo Owolabi, 'yan bindiga sun kai farmaki ofishin 'yan sanda dake Obosi a karamar hukumar Idemili a jihar inda suka sheke 'yan sanda biyu.
'Yan bindigan sun kai farmaki ofishin 'yan sandan a yammacin Laraba inda suka saki dukkan masu laifi dake ofishin sannan suka banka masa wuta, Daily Trust ta wallafa.
Wata majiya mai kusanci da ofishin 'yan sandan tace 'yan bindiga sun isa da yawansu kuma sun kai hari ofishin wurin karfe 11 na dare. Ya bayyana sunayen jami'an da Sifeta James da Awalu.
Asali: Legit.ng