Tambuwal ya jagoranci Gwamnonin PDP domin su hana Gwamnan Kuros-Riba komawa APC
- Kungiyar Gwamnonin PDP ta ziyarci Ben Ayade domin a hana shi sauya-sheka
- Ana rade-radin Gwamnan jihar Kuros Riba ya fara harin sauya-sheka zuwa APC
- An dade ana ta faman takun saka a Jam’iyyar PDP na reshen Jihar Kuros Riba
Gwamnonin jam’iyyar PDP sun huro wuta domin ganin sun hana Mai girma gwamnan jihar Kuros Riba, Ben Ayade, sauya-sheka zuwa APC mai mulki.
Jaridar Daily Trust ta ce kungiyar gwamnonin PDP a karkashin Aminu Waziri Tambuwal sun tafi Kuros-Riba domin ganin Ben Ayade bai bar jam'iyyar PDP ba.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da takwarorinsa na jihohin Delta da Enugu, Sanata Ifeanyi Okowa, Ifeanyi Ugwuany ne su ka ziyarci Garin Kalaba a jiya.
KU KARANTA: Abin da APC za ta yi idan ta na sha'awar mulki - Jaji
Aminu Waziri Tambuwal da tawagarsa na gwamnonin jam’iyyar hamayya sun shafe sa’o’i biyu suna tattauna wa da Dr. Ben Ayade a gidan gwamnatin jihar.
Jam’iyyar PDP ta na neman yadda za ta yi domin ta magance irin abin da ya faru kwanaki a jihar Ebonyi, inda gwamna Dave Umahi ya fice, ya koma APC.
Da yake magana bayan zaman na su, Tambuwal ya ce: “An yi taro hankali kwance, an yi nasara.”
“Mun zo ne a karkashin kungiyar PDP-GF, wanda majalisar NWC ta ba umarni ta zo, ta zauna da abokin aikinmu, Gwamnan Kuros-Riba, Farfesa Ben Ayade.”
KU KARANTA: Boko Haram: Sanatan APC ya bayyana yadda abubuwa su ka cabe
Gwamnan Sokoto ya ce sun zo ne sakamakon abinda ya faru a zaben shugabannin PDP da aka yi a jihar.
Aminu Waziri Tambuwal ya cigaba: “Mun zauna da masu ruwa da tsaki, da yardar Ubangiji, za mu shawo kan matsalolin da ake fama da su, mu kai ga ci.”
Shugaban kungiyar ta PDP-GF ya ce za su gabatar da rahotonsu ga majalisar NWC, inda su kuma za su dauki matakin da ya dace domin dinke wannan baraka.
A jiya kun ji cewa tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce dole a zaben 2023 ayi wa Najeriya sabon lale, ko kuma kasar nan ta wargaje gaba daya.
A cewar Obasanjo, masu buga gangar rabuwar kan al’umma a yau, ba su yin la’akari da sauran kananan kabilu marasa rinjaye da ake da su a fadin kasar nan.
Asali: Legit.ng