Da dumi-dumi: Jami'an Tsaro sun dakile sabon hari da aka kaiwa Ofishin ‘yan sanda na Imo, sun kashe yan daba 8

Da dumi-dumi: Jami'an Tsaro sun dakile sabon hari da aka kaiwa Ofishin ‘yan sanda na Imo, sun kashe yan daba 8

- An kashe wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba wadanda suka so kai hari wani ofishin‘ yan sanda a jihar Imo

- Jami'an tsaro sun kassara su bayan sun dakile harin da suka kai musu a artabun da aka kwashe sa'o'i ana yi

- Jami’an tsaro sun kuma kwato motoci bakwai mallakar ‘yan bindigan

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba a daren Alhamis, 6 ga Mayu, sun yi yunkurin kai hari Hedikwatar’ Yan sanda ta Orlu a jihar Imo.

Jami'an tsaro a wani aikin hadin gwiwa, sun dakile harin kuma sun kashe akalla mutane takwas daga cikin maharan, jaridar The Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Jita-Jitan Hare-Haren Yan Bindiga Ya Kawo Hargitsi a Abuja Yayin da Iyaye Ke Janye Yara Daga Makarantu

Da dumi-dumi: Jami'an Tsaro sun dakile sabon hari da aka kaiwa Ofishin ‘yan sanda na Imo, sun kashe'yan daba 8
Da dumi-dumi: Jami'an Tsaro sun dakile sabon hari da aka kaiwa Ofishin ‘yan sanda na Imo, sun kashe'yan daba 8 Hoto: @Govhopeuzodinma
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa sun kuma kwato motoci bakwai da maharan suka shigo domin ta’asar.

An tattaro cewa an shafe tsawon awanni ana musayar wuta tsakanin ‘yan bindigar da jami’an tsaron.

Artabun ya haifar da firgici yayin da mutane suka rarrabu don kare kansu lamarin da ya sa hanyoyin da ke cikin garin Orlu da kewayensa zama tsit.

Da take bayar da rahoton faruwar lamarin, jaridar The Nation ta bayyana cewa ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ba amma wani babban dan sanda da ba a ambaci sunansa ba ya tabbatar da ci gaban.

An rahoto cewa babban jami’in dan sandan ya ce an tafi da gawarwakin ‘yan fashin da motocin zuwa hedikwatar rundunar ‘yan sanda da ke Owerri.

Ya bayyana cewa ba a kona hedkwatar rundunar 'yan sanda ba kuma ba a kashe kowani jami'in tsaro a harin ba.

KU KARANTA KUMA: Mun shawo kan yan bindiga da suka sace daliban Greenfield, ba zasu kashesu ba: Sheikh Gumi

A gefe guda, ana fargabar mutane biyu sun rasa rayukansu bayan wasu mutane dauke da makamai sun kai hari kan motar banki a kauyen Elemosho da ke kan babbar hanyar Akure-Ondo a karamar hukumar Ondo ta Gabas ta Ondo da yammacin ranar Alhamis.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce ‘yan bindigan sun zo ne a cikin wata motar Lexus, kuma suka afka wa motar da ke kan hanyar zuwa Akure da misalin karfe 5 na yamma sannan suka yi awon gaba da wasu kudade da ba a bayyana yawansu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng