Kano da Wasu Jihohin Arewa 11 Za Su Fuskanci Tsananin Zafi, NiMet Ta Yi Gargadi
- Hukumar NiMET ta fitar da gargaɗi kan hauhawar zafi wanda zai iya haifar da cututtuka a sassa daban-daban na ƙasar Najeriya
- Yanayin zafin zai iya kai wa maki 45°C a arewacin ƙasar, tare da barazanar bullar cutar sankarau, musamman a jihohin Arewa 12
- Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da za su fuskanci matsanancin zafi zuwa 2050
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da sanarwar gargaɗi ga ɗaukacin ƙasar nan game da ƙaruwar yanayin zafi.
NiMet ta yi gargaɗin cewa tsananin zafin da ake ciki zai iya haifar da matsananciyar matsala ga mutane sakamakon dumamar jiki da zafin zai haifar a sassa da dama na ƙasar.

Source: Getty Images
Jihohin Arewa da za su fuskanci tsananin zafi

Kara karanta wannan
Kwamishinan Bauchi da ake zargin ya wawure N4.6bn ya samu izinin zuwa aikin Hajji
A cikin wata sanarwar da NiMet ta fitar, hukumar ta ce ƙaruwar yanayin zafin a faɗin Najeriya na iya kai wasu ga shiga yanayin galabaita saboda zafi, musamman a wasu jihohin Arewa, in ji rahoton BBC Hausa.
Jihohin da NiMet ta bayyana cewa suna cikin hadari na wannan tsananin zafin sun haɗa da:
A cewar sanarwar, sauran jihohin da ba a ambata ba ma na iya fuskantar tasirin zafin, ciki har da sassan kudancin ƙasar.
A hasashen NiMet, yanayin zafin zai iya kai wa maki 40 zuwa 45 a ma'aunin salshiyas a arewacin ƙasar, yayin da tsakiyar ƙasar kuma zai kai tsakanin maki 35 zuwa 38 a ma'aunin salshiyas, a Kudancin ƙasar kuma yanayin na iya kai wa maki 33 zuwa 35.
Hanyoyin kare kai daga zafi
NiMet ta buƙaci mazauna wadannan jihohi da su ɗauki matakan kariya domin rage haɗarin kamuwa da cututtukan da zafi ke haifarwa, in ji rahoton The Guardian.
Hukumar ta ce kasancewar ƙura a sararin samaniya a sassan arewa, idan aka haɗa da matsanancin zafi, zai ƙara haɗarin galabaitar jiki, bugun zafi, da kuma yiwuwar ɓullar cutar sankarau.
NiMet ta ba da shawarar cewa:
"A rika shan ruwa sosai sannan a zauna a wuraren da ke da isasshen iska ko na'urar sanyaya ɗaki idan hakan ta sawwaka, a guji cinkoso a wuraren da ba su da iska, sannan a rage zama ƙarƙashin rana kai-tsaye".

Source: Getty Images
Kariya ga yara da masu bukata ta musamman
Hukumar ta kuma ba da shawarar sanya hula, gilashin kariya daga rana, da kuma shafa man kariya yayin da ake waje, tare da zaɓar tufafi marasa nauyi waɗanda ke ba da damar shigar iska.
NiMet ta buƙaci iyaye da masu kula da yara da su tabbatar da cewa jarirai suna cikin sanyi da kuma isasshen ruwa, sannan ta yi gargaɗin cewa kada a taɓa barin yara a cikin motocin da aka faka.
Bugu da ƙari, an shawarci mazauna yankunan da su rage ayyukan motsa jiki kuma su zauna a cikin gida lokacin da zafi ya fi tsananta, musamman tsakanin ƙarfe 12:00 na rana zuwa 4:00 na yamma.
Wani bincike na Jami'ar Oxford ya nuna Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da za su fuskanci matsanancin zafi nan da shekarar 2050.
Shawarwarin likita ga 'yan Najeriya
A zantawar Legit Hausa da Dr. Shamsu Muhammad daga jihar Katsina, ya ba 'yan Najeriya shawarwari kan yadda za su tafiyar da rayuwarsu a lokutan zafi.'
Likitan ya bada shawara cewa:
"Kamar yadda kuka sani, yanayin zafi da muke fuskanta a yanzu a sassa daban-daban na Najeriya ba abin wasa ba ne. Wannan zafi na iya haddasa matsaloli ga lafiyar jiki, kama daga ciwon kai, jiri, har ma da bugun jini idan ba a kiyaye ba.
"Lallai akwai bukatar a rika shan ruwa akai-akai, wannan shi ne babban makami ga tasirin zafi a jikin mutum. Kar ka jira har sai kaji kishirwa kafin ka sha ruwa. A kuma rage shan abubuwan da ke dauke da sinadarin caffeine kamar shayi mai karfi ko kodin, domin suna sa jiki zubar da ruwa da sauri ta hanyar fitsari."
Dr. Shamsu ya ce akwai bukatar mutane su rika sanya kaya marasa nauyi, masu laushi (kamar auduga), kuma farare ko masu haske, sannan idan za a fita, a rika sanya hula ko amfani da lema don kare kai daga bugun rana.
"Idan ba wai da dalili ba, to a rage fita waje tsakanin karfe 10:00 na safe zuwa 4:00 na yamma, lokacin da rana ta fi zafi. Idan ana cikin gida, a bude tagogi don samun iska mai kyau."
- Dr. Shamsu Muhammad.
Kankara ta zama zinare saboda zafi
A wani labari, mun ruwaito cewa, matsanancin zafin da aka taba tafkawa a jihar Bauchi ya sanya kankara tafi komai daraja a cikin kayan abubuwan da ake amfani da su don neman sauki.
Wani mutumi da ya ke sana'ar sayar da kankarar ya ce a kullum yana samun ribar N30,000 saboda yadda mutane ke dandazon sayen kankarar.
Matsanancin zafin ya sanya kankara tana wahala, kuma ta zama tamkar zinare, domin kuwa yadda ake nemanta ba a neman kayan marmari da sauran abubuwa.
Asali: Legit.ng


