Da Duminsa: Gobara Ta Yi Kaca-Kaca Da Kasuwar Atamfa ta Oshodi Dake Legas

Da Duminsa: Gobara Ta Yi Kaca-Kaca Da Kasuwar Atamfa ta Oshodi Dake Legas

- A jihar Legas, gobara ta lakume wani yanki na kasuwar Cairo dake Oshodi a jihar ta Legas

- Rahotanni sun ce an yi asarar miliyoyin nairori, sai dai babu labarin mutuwa zuwa yanzu

- Tuni aka tura jami'an hukumar kashe gobara ta jihar don shawo kan lamarin cikin gaggawa

Gobara ta lakume wani bangare na kasuwar Cairo a karamar hukumar Oshodi-Isolo da ke jihar Legas.

Jaridar TheCable ta rahoto cewa gobarar ta fara ne da misalin karfe 8 na daren ranar Alhamis, kuma ta shafi bangaren kaya na kasuwar.

Ba a san abin da ya haddasa wutar ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Hukumar Jarrabawar NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2020

Da Duminsa: Gobara Ta Yi Kaca-Kaca Da Kasuwar Atamfa ta Oshodi Dake Legas
Da Duminsa: Gobara Ta Yi Kaca-Kaca Da Kasuwar Atamfa ta Oshodi Dake Legas Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Rahotanni sun ce kayyaki na miliyoyin nairori sun kone saboda da yawa daga cikin shagunan gobarar ta shafa.

A halin yanzu, an tura jami'an hukumar kashe gobara da kuma hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) zuwa wurin da abin ya faru domin shawo kan barkewar gobarar.

KU KARANTA: Najeriya Na Bukatar Karin Tauraron Dan Adam don Yakar 'Yan Bindiga, Inji DG NASRDA

A wani labarin, Ana fargabar mutane biyu sun rasa rayukansu bayan wasu mutane dauke da makamai sun kai hari kan motar banki a kauyen Elemosho da ke kan babbar hanyar Akure-Ondo a karamar hukumar Ondo ta Gabas ta Ondo da yammacin ranar Alhamis.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce ‘yan bindigan sun zo ne a cikin wata motar Lexus, kuma suka afka wa motar da ke kan hanyar zuwa Akure da misalin karfe 5 na yamma sannan suka yi awon gaba da wasu kudade da ba a bayyana yawansu ba.

An harbe mutane uku a yayin aikin, wanda ya dauki mintuna kadan kafin ‘yan bindigan su gudu cikin daji, in ji shaidu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.