Ba abin mamaki bane a wayi gari Boko Haram ta kafa tuta a cikin Aso Rock, Pat Utomi
- Pat Utomi, wani masanin tattalin arziki ya bayyana hasashen fadawar Najeriya hadari nan gaba
- A cewarsa, idan ba a dauki mataki ba, lamarin zai iya kai wa ga Boko Haram su kafa tutarsu a Aso Rock
- Ya kuma bayyana yadda siyasar Najeriya ta zama mummuna ta fuskar kawo wa 'yan kasa sauyi
Wani babban masanin tattalin arzikin Najeriya kuma kwararre a fannin jagoranci, Farfesa Pat Utomi ya yi hasashen makoma mai muni ga Najeriya dangane da halin tsaro da kasar ke fama dashi a yanzu.
A cewar Utomi, matukar ana son Najeriya ta ci gaba da gaske, dole ne a kawar da 'yan siyasa masu aikata laifuka daga jam'iyyun siyasa.
Ya kuma kara da cewa idan yanayin tsaro a kasar bai canza ba, za a iya kai ga matakin da 'yan ta'addan Boko Haram za su kafa tutarsu a cikin Aso Rock, fadar shugabancin Najeriya a Abuja.
KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Hukumar Jarrabawar NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2020
"Abun takaici ne matuka ta fuskoki da yawa. Akwai yawan asarar rayuka, ga tsananin damuwar da ta haifar wa 'yan kasa, saboda yanayin rashin sanin abin da zai faru a nan gaba mai yiyuwa ne makoma ta munana ta kai ga mutuwa.
"Hakan ya bayyana ta hanyar kalubalantar samar da abinci a kasar." Utomi ya fadawa jaridar Sun a wata hira da ta wallafa ranar Alhamis 6 ga watan Mayu.
"Mutane da dama ba za su iya zuwa gonakinsu cikin aminci ba kuma hakan zai iya haifar da hauhawar farashin abinci wanda kan wuce 20% da ba abin mamaki ba ne.
"Hakan na nufin cewa, zai shafi shigar da albarkatun kasa cikin masana'antu, wannan kuwa na nufin za a iya sallamar mutane da yawa daga ayyuka, inda tuni muke da 43% na rashin aikin yi, yayin da rashin aikin yi ga matasa ya haura sama da kashi 45.%"
"Don haka, wadannan alamu ne masu matukar tayar mana da hankali, amma abin takaicin ma shi ne yadda za a iya magance matsalolin tsaro gaba daya, amma mun bar kanmu mu ci gaba da tafiya a irin wannan yanayi.
"Abin takaicin shi ne siyasarmu ba ta da zurfin tunani, tana da matukar gajartan tunani ta hanyar da akasarin kayan aikin siyasa da son zuciya suke tafiya, maimakon yi wa 'yan Najeriya aiki."
"Mun bar wadannan matsalolin su ci gaba da girma, muna ta yaudarar kanmu cewa za a samu sauki, amma a yau wadannan matsalolin sun girma sun kai ga yin barazana ga rayukanmu da amincinmu.
"Duba da yadda lamarin ke tafiya, za mu iya farkawa gobe da ganin cewa mahara sun kafa tutar kungiyar Boko Haram a Aso Rock."
"Dukkanin wadannan abubuwa an yi hasashensu, amma saboda rashawa, idanunmu sun rufe kan wadannan abubuwa. Mun kuma ba da gudunmawa ido rufe zuwa ga halin da muke ciki a yau." Ya kara da cewa
KU KARANTA: Da Duminsa: Gobara Ta Yi Kaca-Kaca Da Kasuwar Atamfa ta Oshodi Dake Legas
A wani labarin, Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kubutar da mutum 13 daga hannun 'yan bindiga da suka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Wata sanarwa da ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar ta fitar a daren jiya Laraba ba ta bayyana lokacin da lamarin ya faru ba.
Mutanen a cewar Kwamishinan Tsaro na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, sun je Bakin Kasuwa da ke Karamar Hukumar Chikun domin yin aikatau a wata gona lokacin da 'yan bindigan suka kai musu harin.
Asali: Legit.ng