Bayan dakatar da Hadiza Bala Usman, za a fara bincike a ma'aikatar NPA
- Biyo bayan dakatar da Manajan Darakta a hukumar NPA, zaa fara bincike a hukumar nan kusa
- Rahotanni sun bayyana cewa, shugaba Buhari ya amince da dakatar da Hadiza Bala Usman
- Gwamnatin tarayya tuni ta hada kwamiti don gudanar da bincike a ma'aikatar ta NPA cikin gaggawa
Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin bincike kan Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa na Najeriya (NPA).
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.
An ruwaito a baya yadda aka dakatar da Hadiza Bala Usman a matsayin Manajan Darakta na hukumar ta NPA.
KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Hukumar Jarrabawar NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2020
Wani hadimin Rotimi Amaechi, Ministan Sufuri ne ya bayyana hakan ga daya daga cikin wakilan Daily Trust, yana mai cewa ba a sanya shi a hukumance ba a lokacin.
Amma a cikin bayaninsa, Shehu ya ce Buhari ya amince da kwamitin bincike kan NPA kuma ya umarci Hadiza Bala Usman da ta sauka a mukaminta.
Sanarwar ta karanta, “Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da shawarar ma’aikatar sufuri karkashin Rt. Hon. Rotimi Amaechi na kafa kwamitin bincike da zai gudanar da bincike a Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwan Najeriya.
“Shugaban kasar ya kuma amince da cewa Manajan Darakta, Hadiza Bala Usman, ta sauka a matsayinta yayin da ake gudanar da bincike. Mista Mohammed Koko zai maye wannan matsayin.
“Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin Daraktan Ma'aikatar Ruwa na ma’aikatar yayin da Mataimakin Darakta na Dokoki a ma’aikatar zai yi aiki a matsayin Sakatare. Sauran membobin kwamitin, Ministan zai nada su.”
KU KARANTA: Da Duminsa: Gobara Ta Yi Kaca-Kaca Da Kasuwar Atamfa ta Oshodi Dake Legas
A wani labarin, Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatad da shugabar hukumar tashoshin jiragen ruwan Najeriya, Hadiza Bala Usman.
A cewar TVC, Buhari ya umurci Mohammed Koko ya dane kujerarta.
Asali: Legit.ng