Gwamnatin Tarayya Ta Yaba da Aikin NYSC, Tace Aikin Yayi Fice Wajen Haɗa Kan Yan Najeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Yaba da Aikin NYSC, Tace Aikin Yayi Fice Wajen Haɗa Kan Yan Najeriya

- Gwamnatin tarayya ta bakin ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, ta yaba da aikin bautar kasa na NYSC

- Gwamnatin tace aikin NYSC na taka muhimmiyar rawa kuma yayi zarra wajen kawo haɗin kai tsakanin yan ƙasa

- Ta ce ya zama wajibi ga dukkan wata gwamnati dake son kawo cigaba da kuma samun nasara ta saka hannun jarinta wajen inganta ayyukan matasa

Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, yace ya zama wajibi mu cigaba da nuna goyon bayan mu ga shirin bautar ƙasa na NYSC domin yanzun shine yayi zarra wajen haɗa kan yan Najeriya.

KARANTA ANAN: Hada Layin Waya da NIN Zai Taimaka Wajen Magance Matsalolin Tsaro, Buhari

Lokacin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da wani ɓangaren aikin matasa yan bautar ƙasa (CDS) da kuma miƙa lambar girmamawa ga darakta janar na NYSC ranar Alhamis, Ministan yace shirin na buƙatar dukkan wani goyon bayan da ya kamata domin ƙara haɗa kan yan ƙasa.

Gwamnatin Tarayya Ta Yaba da Aikin NYSC, Tace Aikin Yayi Fice Wajen Haɗa Kan Yan Najeriya
Gwamnatin Tarayya Ta Yaba da Aikin NYSC, Tace Aikin Yayi Fice Wajen Haɗa Kan Yan Najeriya Hoto: @officialnyscng
Asali: Twitter

Ministan ya ƙara da cewa, duk wata gwamnati ko ƙasa dake son tayi nasara kuma ta samar da shuwagabanni nagari, dole ta saka hanun jarinta wajen inganta rayuwar matasa, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: FG Ta Musanta Zargin Zata Zabtarewa Ma’aikata Albashi, Ta Bayyana Abinda Take Shirin Yiwa Ma’aikatan

Ministan yace:

"A yanzu babu wani aiki da yakai aikin da NYSC ke gudanarwa kawo haɗin kai a Najeriya, shirin na buƙatar duk wani goyon baya da ya kamata domin inganta shi."

"Duk wata ƙasa ko gwamnati matuƙar tana son tayi nasara, ya zama wajibi ta saka hannun jarinta wajen inganta rayuwar matasa, saboda haka yakamata mu taimakawa matasa yan bautar ƙasa."

Anashi jawabin, Darakta Janar na NYSC, Shuaibu Ibrahim, yace abinda yasa aka saka matasa yan bautar ƙasa a cikin CDS shine domin matasan su ko yi kishin ƙasa, kyayykyawar mu'amala da mutane, ƙwarewa a shugabanci da dai sauransu.

A wani labarin kuma Kungiyar Ƙwadugo Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Karta Kuskura Ta Zabtarewa Ma’aikata Albashi

Ƙungiyar ƙwadugo ta ƙasa, NLC, ta gargaɗi gwamnatin tarayya da kada ta kuskura ta zabtarewa ma'aikata albashinsu

Shugaban NLC, Ayuba Waba, shine ya bayyana haka yayin da yake martani kan kalaman da ministan Kuɗi, Zainab Ahmed, tayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel