Alkawarin da Sabon Ministan Makamashi Ya Dauka kan Turakun Wutar Lantarki
- Sabon ministan lantarki da aka naɗa, Joseph Tegbe, ya yi alƙawarin magance yawan faɗuwar turakun wutar lantarki a Najeriya
- Tegbe ya ce a cikin kwanaki 100 na farko, zai mayar da hankali wajen daidaita tsarin da kuma ƙara samar da mitoci
- Ya kuma yi alƙawarin kawo tsauraran dokoki da gyare-gyare domin inganta harkar lantarki a Najeriya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Sabon ministan makamashi, Joseph Tegbe, ya bayyana aniyarsa ta kawo ƙarshen yawaitar faɗuwar layin wutar lantarki na ƙasa idan aka tabbatar da naɗinsa tare da rantsar da shi a hukumance.
Tegbe ya bayyana hakan ne ranar Laraba 6 ga watan Mayu na shekarar yayin da yake amsa tambayoyin sanatoci a zauren majalisar dattawa a lokacin tantance shi domin zama minista.

Source: Instagram
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa ya ce matakin farko na shirinsa na kwanaki 100 zai fi mayar da hankali wajen tabbatar da daidaiton turakun wutar lantarki, wanda ya jima yana haddasa katsewar wuta a sassan ƙasar nan.
Tegbe zai shawo kan faduwar turakun wuta
Jaridar Punch ta wallafa cewar Tegbe ya ce gwamnati za ta kuma ci gaba da rabon mitocin wuta domin rage yawan korafe-korafen da suka shafi caji kudin da ya wuce misali.
Ya ce:
“Ina son mu fara da tabbatar da tsayuwar lantarki. Akwai damuwa sosai kan yawan faɗuwarsa, sannan akwai buƙatar ci gaba da samar da mitoci."
Ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya ta raba mitoci miliyan ɗaya a faɗin ƙasar nan a bara, abin da ya ce ba a taɓa yin irinsa ba a tarihin Najeriya.
Tegbe zai tsaurara matakai kan wutar lantarki
Baya ga batun daidaita turakun wutar, Tegbe ya ce zai kawo tsauraran matakai domin tabbatar da bin ƙa’idoji da ladabtarwa a ɓangaren lantarki.

Kara karanta wannan
NDC ta buɗewa Obi ƙofa, ta mika tikitin takarar shugaban ƙasa ga Kudancin Najeriya
Ya ce akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin gyara matsalolin da suka addabi tsarin samar da wutar lantarki a ƙasar nan.
A kalaman Ministan:
“Muna buƙatar tabbatar da daidaiton turakun wutar a cikin gaggawa. Haka kuma dole ne a tabbatar da bin dokoki da tsauraran matakan aiki domin inganta tsarin."

Source: Facebook
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ne ya naɗa Tegbe a ranar 6 ga watan Mayu, 2026 bayan tsohon ministan lantarki, Adebayo Adelabu, ya yi murabus domin neman takarar gwamnan jihar Oyo.
Najeriya dai ta dade tana fama da matsalar rashin daidaiton lantarki, inda faɗuwar turakun wutar ke yawan jefa al’umma cikin duhu.
Bayanan masana’antu sun nuna cewa tun bayan hawan gwamnatin Tinubu a watan Mayun 2023, an samu faɗuwar turakun wutar fiye da sau 20 zuwa farkon shekarar 2026.
Majalisa ta amince da nadin ministan makamashi
A baya, kun samu labarin cewa majalisar dattawa ta amince da bukatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta nadin sabon ministan lantarki, Joseph Olasunkanmi Tegbe.
Hakan dai ya biyo bayan tantancewar da Majalisar ta yi wa Tegbe, awanni 24 bayan Shugaba Tinubu ya mika sunansa domin ya nada shi a sabon mukamin.
Ya samu wannan dama bayan Bayo Adelabu ya yi murabus daga kujerarsa domin ya tafi neman takarar gwamna a jihar Oyo da sa albarkar shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng
