Sanata ya bukaci majalisa ta dauka tsatsauran mataki a kan mulkin Buhari

Sanata ya bukaci majalisa ta dauka tsatsauran mataki a kan mulkin Buhari

- Francis Fadahunsi, sanata mai wakiltar Osun ta gabas ya bukaci majalisar dattawa da ta dauka mataki a kan gwamnatin Buhari

- Dan majalisar wanda ya jajanta matsalar tsaron da ta addabi kasar nan, ya ce abun takaici ne yadda gwamnoni ke yi wa junansu ta'aziyya kullum

- Ya tabbatar da cewa tunda majalisar tana da karfin ikon nadin mukamai da kuma na tsigewa, toh tayi abinda ya dace

Sanata mai wakiltar Osun ta gabas, Francis Fadahunsi, yayi kira ga majalisar dattawa da ta dauka mummunan mataki domin kawo karshen kalubalen tsaro da ya addabi kasar nan.

Tuni dai yace "Majalisa na da karfin ikon nadawa ko tsigewa", kuma akwai bukatar majalisar dattawa tayi wani abu idan matsalar tsaron kasar nan bata inganta ba.

Kamar yadda wani bidiyonsa ya nuna a ranar Laraba, dan majalisar karkashin jam'iyyar PDP, yayi jawabi yayin da yake bada gudumawa a wata tattaunawa a kan tsaro a zauren majalisar, The Punch ta ruwaito.

Ya ce, "Kowacce rana, zamu cigaba da tashi na minti daya. Abun takaici ne. Ina ganin idan muka cigaba da duba abubuwan da ke faruwa, ba za mu bar wurin nan a yau ba.

KU KARANTA: Da duminsa: Mabiyan Father Mbaka sun fito zanga-zanga bayan bacewarsa a Enugu

Sanata ya bukaci majalisa ta dauka tsatsauran mataki a kan mulkin Buhari
Sanata ya bukaci majalisa ta dauka tsatsauran mataki a kan mulkin Buhari. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta amince da fara amfani da fasahar 5G

"Dole ne mu dauka mummunan mataki idan gwamnati ba za ta iya yin komai ba a kan tsaron kasar nan. Tattalin arziki na durkushewa, don haka dole ne a yi wani abu.

"Dole ne majalisar dattawa tayi aikinta. Muna da karfin ikon nadi ko tsigewa. Ko yana nufin mu duba yatsunmu ne, dole ne mu zauna kuma mu tattauna a majalisar zartarwa sannan mu samo mafita.

"Idan ba haka ba, wata rana muna zaune zamu ga yaro da AK47 kuma kowa sai ya tsere. Amma kuma ba dole dukkanmu su yi sa'a ba. Za mu jira wannan lokacin ne ko yanzu zamu dauka mataki?"

Fadahunsi yayi nadamar yadda gwamnonin jihohi ke yawo zuwa wa juna ta'aziyya saboda matsalar tsaron da ta addabi jiharsa.

Dan majalisar tarayya yace idan gwamnati ta gaza, toh ta sauka daga mulkin.

Ya ce, "Dukkan gwamnonin arewa suna zuwa Zamfara lokaci zuwa lokacin idan aka yi kashe-kashe.

"Don haka dole ne shugaban kasa ya dauka mataki ko kuma gwamnatinsa ta matsa, sabuwa ta cigaba."

A wani labari na daban, Ahmad Gumi, fitaccen Malamin addinin Islama, ya musanta sanin komai a kan N800,000 da aka biya domin a sako daliban makarantar Afaka da aka sace a jihar Kaduna.

A watan Maris ne 'yan bindiga suka kai hari kwalejin gandun daji dake Afaka a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna suka sace dalibai 39.

Amma kuma tuni aka sako 10 daga cikin daliban inda guda 29 aka sako su a ranar Laraba, 5 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel