Ramadan: Tinubu ya rabawa Marayu sama da 4, 000 kayan azumi a Jihar Shugaban kasa

Ramadan: Tinubu ya rabawa Marayu sama da 4, 000 kayan azumi a Jihar Shugaban kasa

- Bola Tinubu ya yi rabon kayan azumin watan Ramadan a Jihar Katsina

- Tsohon Gwamnan jihar Legas ya ba mutum fiye da 4000 kayan shan ruwa

- Tinubu ya yi wannan aiki ne da nufin Musulmai su ji dadin yin buda-baki

Sama da mutum 4, 000 su ka amfana da kayan shan ruwan da babban jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tibubu, ya raba a jihar Katsina.

Jaridar Katsina Post ta rahoto cewa Bola Ahmed Tibubu ya taimaka wa marayu da kuma masu karamin karfi da abin da za su yi buda-baki a Katsina.

Shugaban kwamitin rabon wannan kaya, Alhaji Salisu Mamman, ya shaida wa manema labarai wannan a lokacin da yake gabatar da wadannan kayan.

KU KARANTA: Babachir Lawal ya na marawa takarar Bola Tinubu baya a zaben 2023

Kamar yadda Salisu Mamman ya bayyana, kayan abincin da aka raba sun hada da kilo biyar na shinkafa.

Salisu Mamman ya tabbatar da cewa bayan marayu da marasa hali, za a raba kayan abincin ga yankunan da ‘yan bindiga su ka yi ta’adi a jihar Katsina.

Mamman wanda ya ke da alhakin raba kayan shan ruwan, ya ce Bola Tinubu ya yi wannan abin alheri ne domin Bayin Allah su samu abin yin buda-baki.

Wannan abin alheri ya zo ne a daidai lokacin da aka shiga kwanaki goma na karshen watan Ramadan, an fara hango shirye-shiryen bikin karamar idi.

Ramadan: Tinubu ya rabawa Marayu sama da 4, 000 kayan azumi a Jihar Shugaban kasa
Bola Tinubu Hoto: www.guardian.ng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mabiyan Abduljabbar Kabara sun roki a bude masallacinsu da azumi

Da yake jawabi, Alhaji Salisu Mamman, ya sha alwashin cewa zai yi adalci da gaskiya wajen raba wa wadanda su ka cancanta wadannan kayan karya azumi.

Kwamitin zai bada karfi ne wajen ciyar da marayu da marasa galihu da wadanda rikicin ‘yan bindiga ya jikkata su a kananan hukumomin jihar ta Katsina.

A madadin tsohon gwamnan na Legas, Mamman ya yi kira ga al’umma su cigaba da yi wa shugabanni addu’ar iya magance matsalolin da ke kasar nan.

Yayin da ake gab da shiga watan Ramada, an kaddamar da rabon buhuhunan shinkafa da kayan abinci na tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, a Kano.

Daga baya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya fito ya bayyana cewa ba shi ne ya yi wannan rabo ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel