Yar aji shida a Firamare ta bindige Mai raino da dalibai 2
- Yayin Najeriya ke fama da matsalar yan bindiga, Amurka na fama da matsalar bindiga hannun gama garin mutane
- A wasu jihohin Amurka, ya halatta mutum ya rike bindiga don kare kansa
- Wannan doka ya zama matsala ga kasar dubi ga yadda yara ke daukan bindigogin iyayensu
Wata daliba 'yar aji shida ta bindige dalibai biyu da mai kula da su a wata makaranta dake jihar Idaho, a Amurka ranar Alhamis, 6 ga watan Mayu, 2021.
Jaridar Guardian ta rahoto cewa da kyar aka samu wani Malami ya kwace bindigan daga hannunta.
Shugaban yan sandan yankin, Steve Anderson, ya bayyana cewa dalibar ta harba bindiga a ciki da wajen makarantan.
Anderson ya ki bayyana sunanta kuma ba'a san dalilin da yasa tayi haka ba.
Yan aji shida a Amurka yawanci yan shekaru 11 zuwa 12 ne.
An garzaya da mutum uku da ta harba kuma ana kyautata zaton zasu rayu.
KU KARANTA: Matasan Najeriya 5 da suka daukaka martabar kasar a idon duniya, karamin cikinsu shekararsa 10
KU KARANTA: Jerin kasashe 20 mafi shugabannin kwarai a duniya, Rahoton Bincike
Dirakta a asibitin Eastern Idaho regional medical center, Dr Micheal Lemon, ya bayyana cewa an cire harsashin dake jikin mai kula da daliban kuma an fara jinya.
A cewarsa, harsashin ya sami mai kulan a kafa.
Amma daliban biyu na asibiti har yanzu kuma da yiwuwan a yiwa daya ciki aikin Tiyata, Dr Lemon ya kara.
"Yau mun ga abin tsoro da makaranta zai iya fuskanta," wani jagora a yankin, Chad Martin ya bayyana.
A wani labarin kuwa, a ranar Talata, Sakataren ƙasar Amurka, Antony J. Blinken, ya ya gana da shugaba Buhari da kuma ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama.
Mutanen uku sun tattauna akan abubuwa da dama, waɗanda suka haɗa da; yadda zasu haɗa kai wajen yaƙar ta'addanci da rashin tsaro, gyaran ɓangaren lafiya, bunƙasa tattalin arziƙi da sauransu.
Hakanan kuma shugaba Buhari ya tattauna da sakataren kan yadda za'a bunƙasa kasuwanci tsakanin ƙasar Amurka da Najeriya.
Asali: Legit.ng