Latest
A kalla mutum 15 ne suka rasa rayukansu a kauyen Koya dake karamar hukumar Minjibir ta jihar Kano bayan zargin barkewar cutar amai da gudawa a yankin dake Kano.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA ta bankaɗo wadu gurɓatattun mutane dake safarar miyagun ƙwayoyi a yanar gizo, ta damke mutum biyar a Abuja.
Wasu yan bindiga sun kashe wani jigo a garin Goƙkofa dake karamar hukumar Jema'a jihar Kaduna, matarsa da sirikarsa. Kwamishin tsaron jihar ya tabbatar da haka.
Kungiyar tuntuba ta arewa ta bayyana adawarta ga biyan kudin fansa ga 'yan bindiga. Kungiyar ta ce tana goyon bayan a tattauna amma ba ta goyon bayan fansa.
Rokan da kasar Sin ta harba sararin samaniya a Afrilun 2021 ya dawo duniya yau Lahadi 9 ga Mayu cikin tekun Indiya kuma ya kama da wuta, hukuma a Sin ta bayyana
Musulmi na farko da ya taɓa riƙe kujerar magajin garin Landan, Ahmad Khan, ya sake lashe zaɓe a karo na biyu. Khan ya zama magajin garin Landan ne tun 2016.
Wasu yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba, sun ƙone ofishin hukumar yan sanda dake kasuwar Ubani, ƙaramar hukumar Bende, jihar Abia da sanyin safiyar Lahadi.
Sanannen abu ne cewa Ahmed Musa na ɗaya daga cikin yan wasan Najeriya masu arziki duba da kuɗin da ɗan wasan gaban ya samu tun lokacin da ya fara harkar ƙwallo.
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da samamen da ta kai ga kame wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne a jihar Kano a ranar Asabar, 8 ga watan Mayu.
Masu zafi
Samu kari