Gwamnonin da Wa'adinsu Zai Kare a 2027 da Suke Harin Tafiya Majalisar Dattawa
FCT, Abuja - A shekarar 2027 wasu daga cikin gwamnonin jihohin Najeriya za su kammala wa'adinsu na biyu a kan kujerar mulki.
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Wasu daga cikin wadannan gwamnonin da wa'adinsu zai kare, sun bayyana aniyarsu ta neman takarar sanata domin zuwa majalisar dattawa.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro gwamnonin da ke harin tafiya majalisar dattawa a shekarar 2027 bayan kammala wa'adin mulkinsu.
Gwamnonin jihohi 12 za su kammala wa'adinsu
Gwamnoni 12 ne daga cikin gwamnoni 36 masu ci suke kan wa’adinsu na biyu kuma na ƙarshe a ofis.
Daga cikin wannan adadin, mutum 10 za su kammala wa’adin shekaru takwas da kundin tsarin mulki ya ba su a ranar 29 ga watan Mayu, 2027.
Takwas daga cikin gwamnonin da abin ya shafa mambobi ne na jam’iyya mai mulki ta APC, yayin da biyu; Seyi Makinde na jihar Oyo da Bala Mohammed na jihar Bauchi, suke a jam’iyyun adawa na PDP da APM.
Wasu gwamnoni za su nemi kujerun sanata
Tuni dai wasu daga cikin gwamnonin da wa'adinsu zai kare a 2027, suka bayyana aniyarsu ta fitowa takarar sanata.
Wasu daga cikin wadannan gwamnonin har fom din neman tsayawa takara sun riga sun mallaka.
Ga jerinsu a nan kasa:
1. Abdullahi Sule (Nasarawa)
Gwamna Abdullahi Sule ya fito fili ya amince da cewa akwai matsin lamba daga masu ruwa da tsaki na su tursasa shi takarar kujerar sanatan Nasarawa ta Arewa a 2027.

Source: Facebook
Jaridar The Guardian ta ce yayin da yake jawabi ga mambobin majalisar zartarwa ta jiha, ya bayyana cewa tun farko ya cire ran sake tsayawa wani zaɓe, amma yana sake nazari ne saboda yawan koke-koke daga shugabannin siyasa da na gargajiya.
“Ganin duk matsin lambar da ke fitowa daga shugabanninmu, na yi musu alƙawarin zan tsaya takara idan lokaci ya yi.”
- Gwamna Abdullahi Sule
2. Mai Mala Buni (Yobe)
Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana sha’awar sa ta neman kujerar sanatan Yobe ta Gabas a babban zaɓe mai zuwa.

Source: Twitter
Gwamnan, wanda tuni ya karɓi fom ɗin tsayawa takarar, ya ce ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan ƙaruwar matsin lamba daga masu ruwa da tsaki na siyasa da magoya baya a cikin jam’iyya mai mulki ta APC.
Jaridar Daily Trust ta ce yayin karɓar fom ɗin na gani ina so da na tsayawa takara da ƙungiyar masu riƙe da madafun ikon siyasa da na gwamnati na shiyyar 'Zone A' a Yobe suka saya masa, ya bayyana cewa:
“Ba zan iya gode muku yadda ya kamata ba, kuma na yi alƙawarin ci gaba da yi wa mutanenmu hidima cikin jajircewa."
3. Bala Mohammed (Bauchi)
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar sanatan Bauchi ta Kudu a 2027, jaridar PM News ta kawo rahoton.

Source: Facebook
Gwamna Bala wanda ya taba sanata a 2007 ya kuma bayyana cewa bai da burin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.
“Ba ni da sha’awar tsayawa takarar shugaban ƙasa; mun goyi bayan raba mulki zuwa Kudu ne domin adalci."
“Na yanke shawarar tsayawa takarar sanata ne saboda mutanen Bauchi ta Kudu sun buƙace ni. Matuƙar ina raye kuma ina da lafiya, zan amsa wannan kiran.”
- Gwamna Bala Mohammed
4. Muhammadu Inuwa Yahaya (Gombe)
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana aniyarsa ta neman takarar sanatan Gombe ta Arewa.
A cikin wata sanarwa da kakakinsa, Ismaila Uba Misilli, ya sanya a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 3 ga watan Mayun 2026, ya bayyana cewa an zabi Gwamna Inuwa a matsayin dan takarar maslaha na APC a kujerar sanatan Gombe ta Tsakiya.

Source: Facebook
5. Ahmadu Umaru Fintiri (Adamawa)
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya tabbatar da cewa zai fito takarar kujerar sanatan Adamawa ta Arewa a zaben 2027.
A wani rubutu a shafinsa na X a ranar Lahadi, 3 ga watan Mayun 2026, Gwamna Fintiri ya bayyana cewa ya amsa kiran da ake yi masa domin tsayawa takarar kujerar a karkashin inuwar APC.

Kara karanta wannan
Zambar N1.5bn: Gwamnatin Kano za ta hukunta jami'an da suka tsakure albashin ma'aikata

Source: Twitter
6. Dapo Abiodun (Ogun)
Gwamnan jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun, ya bayyana aniyar tsayawa takarar kujerar sanatan Ogun ta Gabas a Majalisar dattawa.

Source: Twitter
Jaridar Tribune ta ce ya bayyana hakan ne a daren Talata, 28 ga Afrilun 2026, yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na shiyyar Ogun ta Gabas da aka gudanar a Iperu Remo.
Abiodun, yayin da yake jawabi a taron, ya yi alƙawarin ba wa mutanen Ogun ta Gabas wakilci na gari a majalisar dattawa.
APC ta tsayar da dan takarar gwamna a Gombe
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta zabi dan takarar gwamna a jihar Gombe ta hanyar amfani da tsarin maslaha.
Jam'iyyar APC ta zabi Jamilu Isiyaku Gwamna a matsayin dan takararta na gwamnan Gombe a zaben shekarar 2027.
Hakazalika, APC ta zabi 'yan takararta na kujerun majalisar dokoki ta jiha, majalisar wakilai da majalisar dattawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


