Dukiyar AbdulSamad Rabiu Ta Tumbatsa, Ya Zama na 2 da Ya Fi Kowa Arziki a Afrika
- Attajirin Najeriya, Abdulsamad Rabiu ya samu karuwar riba a kamfanoninsa da ke sassa daban-daban na Najeriya, wanda ya sa arzikinsa ya karu
- Kididdiga ta tabbatar da cewa arzikinsa ya kai Dala biliyan 19 bayan ya samu ƙarin Dala biliyan 8.88 cikin shekara guda na kasuwancinsa
- Nasarar da fitaccen attajirin ya samu a rukunin kamfanin BUA da ribar BUA Foods sun taimaka wajen haɓakar dukiyarsa har ya zarce Johann Rupert
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Hamshaƙin attajirin Najeriya, Abdulsamad Rabiu, ya zama mutum na biyu mafi arziki a nahiyar Afrika bayan samun gagarumar ƙaruwa a dukiyarsa cikin shekarar 2026.
Rahotanni sun nuna cewa dukiyar Abdulsamad Rabiu yanzu ta kai Dala biliyan 19, bayan da ta ƙaru da Dala biliyan 8.88 tun farkon shekarar nan.

Source: UGC
Business Insider Africa ta wallafa cewa wannan ci gaba ya sa ya zama attajirin da ya fi kowa samun ƙarin arziki a Afrika cikin wannan shekara.
Arzikin AbdulSamad Rabiu ta karu
A halin yanzu, Abdulsamad Rabiu, na biye ne kawai bayan attajirin Afrika mafi arziki, kuma shugaban kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote.
Hakan na nufin ya wuce attajirin ƙasar Afrika ta Kudu, Johann Rupert, wanda dukiyarsa ta ragu zuwa Dala biliyan 17.7.
Bayan sabon matsayinsa, Abdulsamad Rabiu, ya koma matsayi na 138 a jerin attajiran duniya, lamarin da ke nuna irin saurin bunƙasar dukiyarsa cikin ɗan lokaci.

Source: UGC
A makon da ya gabata, an ƙiyasta dukiyarsa kan Dala biliyan 15.9, amma ci gaba da tashin darajar hannayen jarinsa ya sa ya ƙara samun babban matsayi a duniya.
Tun farko a shekarar nan, attajirin nan Natie Kirsh ne ya fi kowa samun ƙaruwar dukiya a AfrIka, sai dai ci gaban Abdulsamad Rabiu, ya sauya tsarin jerin masu arziki a nahiyar.
Yadda arzikin Abdulsamad Rabiu ya habaka
Masana tattalin arziki na danganta ƙaruwar dukiyar Abdulsamad Rabiu, da irin gagarumar nasarar da kamfanin BUA Foods ya samu duk da matsin tattalin arzikin Najeriya.
Rahoton kuɗin shiga na zangon farko na shekarar 2026 ya nuna cewa ribar kamfanin bayan haraji ta ƙaru da 14% zuwa Naira biliyan 142.32, idan aka kwatanta da Naira biliyan 125.28 a makamancin lokacin bara.
Ko da yake kuɗIn shiga sun ragu da 11% zuwa Naira biliyan 394.6 sakamakon saukar farashi da daidaituwar canjin kuɗi, kamfanin ya ci gaba da samun riba mai yawa.
Ribar ɗanyen kaya ta ƙaru da 9% zuwa Naira biliyan 175.65 saboda raguwar kuɗin sarrafawa da inganta aiki. Haka kuma, ribar gudanarwa ta ƙaru da 11% zuwa naira biliyan 154.6.
Kamfanin AbdulSamad Rabiu ya tallafa wa dalibai
A baya mun wallafa cewa kamfanin simintin BUA ya ware jihohi uku a Arewacin Najeriya inda ya tallafawa dalibai da dama wajen samun karatun zamani domin su samu damar inganta rayuwarsu.
Majiyoyi sun ce aƙalla an ba ɗalibai 200 daga jihohin da aka zaba tallafin karatu na ₦200,000, domin ƙarfafa ilimi a yankin Arewa, wanda ake ganin zai tallafa masu wajen saukaka samun ilimi.
BUA ya ninka tallafin daga ₦100,000 zuwa ₦200,000 saboda hauhawar farashi, yana kuma sa ran ɗaliban da suka ci gajiyar za su inganta karatunsu da a nan gaba zai bunkasa rayuwarsu baki daya.
Asali: Legit.ng


