Daga Rantsar da Mataimakin Gwamna, 'Yan Daba Sun Hallaka Matasa 5 a Kano
- Hankula sun tashi a jihar Kano awanni kadan bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da Murtala Sule Garo a matsayin mataimakinsa
- Rahotanni sun tabbatar da cewa an kashe matashi Nura Ribadu a harin da ake zargin ’yan daban siyasa sun kai masa hari har cikin wani asibiti
- Lamarin ya faru ne a harabar Kano Medical Centre bayan rantsar da sabon mataimakin gwamna inda aka ga matasa rike da mugayen makamai
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – An kashe wani matashi mai suna Nura Ribadu bayan wani hari da ake zargin wasu ’yan daba masu alaƙa da siyasa ne suka kai a harabar Kano Medical Centre da ke kan titin Race Course a jihar Kano.
Rahotanni na farko sun nuna cewa lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar, Murtala Garo, lamarin da ya haifar da firgici da tashin hankali a yankin.

Source: Original
A rahoton da Premier Radio ta wallafa a shafin Facebook, mamacin, wanda ake kyautata zaton mazaunin unguwar Dandago ne a karamar hukumar Gwale, ya rasu ne sakamakon raunukan da ya samu yayin harin da aka kai masa a cikin harabar asibitin.
An kashe matasa a birnin Kano
Rahotanni sun bayyana cewa ba wai Nuhu kawai aka kashe ba, har da karin wasu matasa hudu a jihar Kano. Kuma an birne mutane uku a ranar Talata 5 ga watan Mayu, 2026.
Ana sa ran za a birne sauran mutane biyu da ake cewa an kashe, yayin da iyayen wadanda aka hallaka suka bayyana cewa ba za su yafe ba.
A bangaren iyalan mamacin, mahaifin daya daga cikin wadanda aka kashe, Alhaji Abba Usman Dandago, ya bayyana takaicinsa kan yadda ake tafiyar da siyasa a wannan lokaci.

Source: Facebook
Ya ce:
"Rayuka ake nema ba wai a taimaki talaka a ke nema ba iya abin da za a baka, a dauki babur ne a baka. A yi ta yi maka ihu a yi maka murnar babur N500,00, N600,000. Shi nawa ya sata? Nawa ya diba?
"Harkar nan ta siyasa kowa yana so ya yi ta, amma ba ta da amfani a wannan zamanin, siyasa ta zama yanzu ba ta da amfanin komai. Yanzu da manyan da yaran duk ran mutane suke nema."
An yi wa manyan Kano Allah Ya isa
Haka kuma Rabiu Sabiu Dandago, wanda ya ce ya birne dansa da aka kashe a wannan lamari, ya yi kakkausar suka tare da yin addu’ar fushi ga shugabannin da suka gaza dakatar da irin wannan tashin hankali.
Ya ce:
"Yau ga shi an kashe min dana, an kashe yaro, dana ne shi ma Nura. Ina ji ina gani duk an kashe min su, su biyu."
"Ba abin da ya yi yaron nan, kasuwa ya ke zuwa. Kullum zai tafi kasuwa, wallahi jiya ni da shi na ke masa magana, na ce mahaifiyarka ta dogara da kai, kana zuwa kasuwa, ka tsaya ka ba ta gudunmawa."
"Gaskiya Allah Ya isa, Wallahi Allah Ya isa. Da shi gwamna da duk wanda ya ke da hannu a lalata wannan al'amarin siyasa, wallahi Allah isa. Kuma bukatarsu ba za ta biya ba."
An rantsar da mataimakin gwamnan Kano
A baya, mun wallafa cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da Mutala Sule Garo a matsayin mataimkin gwamna a wani taro da aka shirya yau Talata, 5 ga watan Mayu, nas shekarar 2026.
Tsohon shugaban APC na kasa, Dr Abdullahi Ganduje da Malam Ibrahim Shekaru na cikin manyan bakin da suka halarci bikin rantsar da Garo a yayin da aka rika taya shi murna samun mukamin.
Wannan na zuwa ne bayan Majalisar dokokin Kano karkashin jagorancin Rt. Hon. Jibril Isma'il Falgore ta tantance tare da amincewa da shi bayan Aminu AbdulSalam Gwarzo ya ajiye aiki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


