'Yan ta'addan ISWAP sun tarwatsa sansanin soji a jihar Borno

'Yan ta'addan ISWAP sun tarwatsa sansanin soji a jihar Borno

- Mayakan ta'addanci na ISWAP sun kai mugun hari sansanin sojojin Najeriya dake Damboa a Borno

- An gano cewa sun kai harin a ranar Alhamis, 6 ga watan Mayu inda suka tarwatsa sansanin sojin

- Damboa gari ne dake da nisan kilomita 87 daga Maiduguri kuma yana da kusanci da mugun dajin Alagarno

Mummunan harin da kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta kai yayi sanadin tarwatsewar sansanin sojojin Najeriya dake Damboa a jihar Borno dake arewa maso gabas, HumAngle ta ruwaito.

Damboa na kusa da sashin kudancin jihar Borno, cibiyar 'yan ta'addan Boko Haram a Najeriya kuma kusa da mugun dajin Alagarno.

Hedkwatar karamar hukumar tana da nisan kilomita 87 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Sun kai harin ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Mayu inda suka watsa runduna ta 25 da aka tura Bulabulin. Mayakan sun bayyana a motocin yaki ne da babura.

KU KARANTA: Kayatattun Hotunan katafaren filin jiragen sama na China ya bar mutane baki bude

'Yan ta'addan ISWAP sun tarwatsa sansanin soji a jihar Borno
'Yan ta'addan ISWAP sun tarwatsa sansanin soji a jihar Borno. Hoto daga @HumAngle
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shigar Boko Haram Abuja: 'Yan sandan FCT sun magantu, an fara sintiri babu kakkautawa

HumAngle ta gano cewa miyagun 'yan ta'addan sun samu nasarar kwace sansanin.

Lamarin da ya faru a ranar Alhamis na daga cikin miyagun hare-haren da 'yan ta'addan ke kaiwa sansanin sojoji a garuruwan Borno da Yobe.

Hakan kuwa ya kawo karantsaye da tsaiko ga tallafi tare da taimakon da al'umma ke kaiwa jama'a a yankunan, wanda kuwa suke matukar bukata.

A wani labari na daban, rundunar sojin Najeriya ta sauyawa rundunar Operation Lafiya Dole dake yakar Boko Haram suna zuwa Operation Hadin kai. Wannan ne suna na uku da aka sanyawa rundunar tun bayan kafa ta.

Tsohon shugaban rundunar sojin Najeriya, Tukur Buratai a 2015 ya sauya mata suna daga Operation Zaman Lafiya suwa Operation Lafiya Dole, wanda yace hakan yayi shi ne domin tabbatar da cewa dole ne a samu zaman lafiya a yankin arewa maso gabas.

Amma Mohammed Yerima, mai magana da yawun rundunar, a wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a, ya ce sauya sunan zuwa hadin Kai na nufin zama tsintsiya daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: