'Yan Bindiga Sun Afkawa Motar Kudi, Sun Kwashi Makudan Kudade
- Wasu 'yan bindiga sun tare motar banki dauke da kudi sun kwashe wasu adadin kudade
- An ruwaito cewa, sun harbe mutane uku yayin harin, sun kuma yi awon gaba zuwa daji
- Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma bayyana cewa tana kan bincike
Ana fargabar mutane biyu sun rasa rayukansu bayan wasu mutane dauke da makamai sun kai hari kan motar banki a kauyen Elemosho da ke kan babbar hanyar Akure-Ondo a karamar hukumar Ondo ta Gabas ta Ondo da yammacin ranar Alhamis.
Wadanda suka shaida lamarin sun ce ‘yan bindigan sun zo ne a cikin wata motar Lexus, kuma suka afka wa motar da ke kan hanyar zuwa Akure da misalin karfe 5 na yamma sannan suka yi awon gaba da wasu kudade da ba a bayyana yawansu ba.
An harbe mutane uku a yayin aikin, wanda ya dauki mintuna kadan kafin ‘yan bindigan su gudu cikin daji, in ji shaidu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA: Sojojin Najeriya Sun Yi Nasarar Ceto Mutane 13 a Hannun 'Yan Bindiga a Jihar Kaduna
“Daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su yana raye yayin da babu tabbacin ko sauran biyun suna raye,” in ji wani ganau.
Mazauna sun kuma tsere cikin daji sakamakon harbe-harben da suka faru yayin harin..
Motoci biyu daga cikin uku a ayarin motocin cike suke da harsasai a harin.
Shaidan ya kara da cewa an gayyaci jami'an Hukumar Tsaro ta Jihar Ondo ta Amotekun zuwa wurin da abin ya faru sannan suka dauki mutum daya da lamarin ya rutsa da shi zuwa asibiti.
Kwamandan Amotekun, Adetunji Adeleye, ya tabbatar da faruwar lamarin.
"Lokacin da muka samu labari, mutanena sun je wurin sai suka samu da daya daga cikin mutanen da aka harba a wurin kuma mun kai shi asibiti."
Babu wanda ya jikkata, in ji shi.
Hakazalika, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Mista Tee-Leo Ikoro ya ce 'yan bindigan sun gudu kafin ’yan sanda su iso wurin.
Ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike a kan lamarin sannan kuma jami'an 'yan sanda daga rundunar sun fara bibiyar barayin.
KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Hukumar Jarrabawar NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2020
Wata sanarwa da ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar ta fitar a daren jiya Laraba ba ta bayyana lokacin da lamarin ya faru ba.
Mutanen a cewar Kwamishinan Tsaro na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, sun je Bakin Kasuwa da ke Karamar Hukumar Chikun domin yin aikatau a wata gona lokacin da 'yan bindigan suka kai musu harin.
Asali: Legit.ng