Latest
Huhu John Gwamna ya bayyana cewa Musulmai ne suka taimaka masa wajen gina aikinsa, yana mai cewa bai taɓa fuskantar wariyar addini a gwamnatin El-Rufai ba.
Dan takarar shugaban kasa a SDP a zaben shekarar 2027 da ke tafe, Adewole Adebayo, ya yi alkawarin samar da hasken rana ga kowane gida cikin watanni 11.
Sheikh Ahmad Gumi ya yi kira da a yi garambawul ga kotunan Shari’a a Kaduna, yana mai cewa jinkirin shari’ar auratayya na ƙara tsananta wa mata a gidaje.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa karin kudin FAAC da jihohi ke samu ba gaskiya ba ne domin faduwar darajar naira da hauhawar farashi sun maida kudin marasa amfani.
Gwamnatocin ADC a Arewa maso yamma za su goyi bayan rage kudin fetur, karin albashi da samar da tsaro a yankin. Kai albashi fiye da N100, 000 na cikin alkawuransu.
Oluremi Tinubu ta roƙi ’yan Kudu maso Gabas su sake zaɓar Bola Ahmed Tinubu a 2027, yayin da sanatan ta ƙarfafa mata 2,500 a Imo da tallafin N100,000.
Ƙungiyar Houthi ta kai hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan biranen Khamis Mushait, Abha da Jizan a kudu maso yammacin Saudiyya.
Dan takarar gwamnan APC, Kingsley Chinda ya fara kamfen ɗin gwamnan Rivers, inda ya yi alkawarin yi wa jihar hidima da tsoron Allah da ƙaunar jama’a.
Yan takarar gwamnan jam'iyyar ADC) a jihohi bakwai na yankin Arewa maso Yamma sun bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya janye matakin cire tallafin fetur.
Masu zafi
Samu kari